05/08/2023
CIKIYA! CIKIYA! CIKIYA!
Jama'a, Assalamu Alaikum.
Wannan yara da kuke gani an tsince su ne jiya da daddare a guraren hanyar shiga Unguwar Rimi, ta bayan gidan man A.A. Rano dake nan cikin garin Jos.
Babbar ta ce sunan ta Nana, ƙaramar kuma Islam, sannan shi kuma yaron da ke hannun su sunan shi Nasiru.
Nana ta ce sun taho da maman su ne daga jihar Jigawa, sannan maman tace wai za su je suna a ZUNTU.
Mutanen yankin sun ce tun misalin ƙarfe 9 na daren jiya Juma'a, 4 ga watan Agustan 2023 a ka ga yaran a zaune. To amma bawan Allahn da ya haɗa mu da su, wanda kuma gidan shi na kusa da gurin da aka ajiye yaran ya ce mana mai gadin gidan man A.A. Rano ya kira shi ne da misalin ƙarfe 11 na dare don sanar da shi halin da ake ciki.
Nana dai ta ce maman su ce ta ajiye su a gurin wai su jira ta, za ta je ta siyo mu su biredi tun da yamma.
A saboda haka mu ke rokon don girman Allah, al'umma su yita yaɗa wannan rubutu da hoto ko Allah zai sa ƴan uwan su zasu gani.
Ku tuna, shi dai “YARO NA KOWA NE".
ALLAH YA BAYYANA MANA ƳAN UWAN WANNAN YARA. AMIN THUMMA AMIN.
Za ku iya tuntubar lambobin waya kamar haka domin neman ƙarin bayani akan inda yaran su ke:
Haruna Umar (07062579831)
Ibrahim Idris Badamasi (08031866089)
Baban Jos (09163994346)