17/07/2026
Tasirin Kalmar “ALLAH YA ISA”ga Wanda Aka Zalunta
Kalmar “Allah ya isa” (wato: Allah Ya isa mini, Shi ne mafi alherin Wakili) tana daga cikin manyan kalmomin tawakkali da mika al’amari ga Allah Maɗaukakin Sarki. Idan wanda aka zalunta ya furta ta da cikakkiyar imani da gaskiya, tana da tasiri mai girma a rayuwarsa.
Wanene wanda aka zalunta?
Wanda aka zalunta shi ne wanda aka tauye masa haƙƙinsa ba tare da wani laifi ba. Zalunci yana iya kasancewa:
* Zalunci a cikin aure.
* Zalunci a kasuwanci.
* Zalunci wajen aiki.
* Zalunci tsakanin ’yan uwa.
* Zalunci daga shugabanni.
* Zalunci ta hanyar ƙarya, cin mutunci, ko cin amana.
1. Shawara ga wanda aka zalunta
* Ka yi haƙuri.
* Ka ci gaba da addu’a.
* Ka guji ramuwar gayya ta haram.
* Ka nemi haƙƙinka ta halal idan hakan yana yiwuwa.
* Ka yawaita cewa:
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil.”
* Ka yi kyakkyawan zato ga Allah, domin Allah ba Ya watsi da haƙƙin wanda aka zalunta.
Wanda aka zalunta yana nuna cewa ya miƙa al’amarinsa gaba ɗaya ga Allah, domin Shi ne Mai adalci wanda ba Ya zaluntar kowa.
حَسْبُنَا اللَّهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ
“Allah Ya isa mana, kuma Shi ne mafi alherin Wakili.”
(Suratu Āli ’Imrān: 173)
2. Tana kwantar da zuciya
Kalmar tana kawar da fargaba da baƙin ciki, tana sanya nutsuwa da haƙuri a zuciyar wanda aka zalunta, domin ya san cewa Allah yana sane da halin da yake ciki.
3. Tana jawo taimakon Allah
Duk wanda ya dogara ga Allah da gaskiya, Allah yana taimakonsa, yana buɗe masa hanyoyin mafita daga inda bai zata ba.
4. Tana kare wanda aka zalunta
Allah yana kare bayinsa masu tawakkali, kuma Yakan mayar da makircin azzalumai a kansu idan Ya so.
5. Addu’ar wanda aka zalunta ba ta da shamaki
Annabi ﷺ ya ce:
“Ku ji tsoron addu’ar wanda aka zalunta, domin babu shamaki tsakaninta da Allah.”
Saboda haka, idan wanda aka zalunta ya ce “Allah ya isa” cikin gaskiya, yana neman hukuncin Allah ne, ba wai yana neman ɗaukar fansa da kansa ba.
6. Tana zama sanadin nasara
Allah yana ba wanda aka za