17/02/2026
Kanku Musa (Mansa Musa): Mutum Mafi Arziki A Tarihin Duniya
Sarkin daular Mali, Kanku Musa ya kasance mutum mafi ƙarfin arziki da aka taba samu a duniya. Wadatarsa ta ba shi damar mayar da Timbuktu cikin birni mai ban mamaki. Ya yi sarauta tsakanin shekarar 1313 zuwa 1337.
An haifi Kanku Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Koda yake ana yawan kiran shi Kankan Musa, amma ainihin sunansa ‘Kanku’. Wannan sunan mata ne da ya samo asali daga dangin mahaifiyarsa. Wasu daga cikin manyan ƙabilun wancan lokacin sun fi danganta yaro da ɓangaren uwa, don haka maza ma suke ɗaukar sunan mahaifiyarsu.
A cikin shekarar 1313, bayan rasuwar wansa Sarki Abu Bakr II, Musa ya zama shugaban Daular Mali. A lokacin mulkinsa na tsawon shekaru da dama, ya yaɗa al’adun Musulunci a kewayen ƙasar Mali, kuma daular ta zama ɗaya daga cikin waɗanda s**a cigaba a duniya.
Kanku Musa ya fito ne daga gidan sarauta na su Keita waɗanda s**a yi mulkin Mali tsawon ƙarnoni da yawa. Ya kasance sarki mai wadata wanda ya gina daula mai Karfin faɗa a ji, kuma wacce ta bunƙasa. Bisa ga bayanan al’adar baka, kakansa Abu Bakr na farko, Kani ne ga Sunjata Keita wanda ya kafa Daular Mali. Sarautar Musa ta haska daular Mali a duniya.
A zamanin mulkin Musa, wataƙila kasar Mali ce ta kasance mai samar da zinari mafi girma a duniya, kuma ana ɗaukar Musa ɗaya daga mutane mafi arziki a tarihi. Koyaya, masu sharhi na zamani irin su mujallar Time sun kammala da cewa babu ingantacciyar hanyar da za ta ƙayyade arzikin Musa. Amma Kuma mujallar marca tace Gabaɗaya, kiyasin dukiyar za ta kai kusan dala biliyan 400
A shekarar 1324, Kanku Musa ya tafi aikin hajji a Makka. Ayarinsa ya ƙunshi mutum dubu 60 da bayi dubu 12 da dogarai da ke sanye da kayan kawa da sanduna na zinare waɗanda kuma ke kula da dawakai da kayansu.
Wannan ƙasaitaccen rangadin ya sa ya zama sananne, musamman a Yammacin Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya. A cikin kowane gari da ya ya da zango, Musa ya kasance mai karamci sosai kuma ya yi ta ba da ky