Baffah Isa Bajoga

Baffah Isa Bajoga Allah kasa Ranar da zamu koma gareka tafi ko wacce Rana farinciki a garemu 🤲

24/12/2025

Alhamdu lillah 🤲

RABI'UL AWWAL... Wannan ba wata ne kawai da yake juyawa da tafiyar kalanda ba, ko kwanaki da suke tafiya a cikin shekaru...
24/08/2025

RABI'UL AWWAL...

Wannan ba wata ne kawai da yake juyawa da tafiyar kalanda ba, ko kwanaki da suke tafiya a cikin shekaru ba. A wannan watan aka haifi mutumin da ba sarki ba ne, ba attajiri ba ne; maraya ne kawai da ya zama mafi girman halittu.

Idan muka kalli haihuwa da rayuwar Manzon Allah (saw), sai mu ga Allah yana koya mana tawadhu'u. Bawan Allah ne da aka haifa maraya amma ya zama uba ga duniya, aka haifa cikin rashi amma samunsa ya zama arziki mafi girma. Tamkar Rabi'ul Awwal na gaya mana cewa ba bukatar farawa cikin samu domin a isa zuwa ga nasara. Abin da ake bukata shi ne kyakkyawar zuciya, harshe na gaskiya, da ruhi tsarkakke.

Maulidin Manzon Allah (saw) ba wai gurin tarihi ba ne kawai. Wata munasaba ce a duk shekara da take sakawa mu tambayi kanmu: Me muka yi da sakon Manzon Allah? Shin muna haskaka tafiyarmu da rayuwarsa? Me muke aikatawa da rahamarsa? Domin Allah ne ya gaya mana cewa Manzon Allah rahama ne ga talikai - mutane, aljanu, dabbobi, musulmi da wanda ba musulmi ba.

Rabi'ul Awwal ya zo domin ya koya mana cewa maulidi na hakika bai tsaya a cikin taruka da wakoki ba. Ya zo ne domin ya tuna mana cewa hakikar maulidi shi ne dabbaka rahamar Manzon Allah ga dukan halittu. Ta yadda za mu kalli matalauci da idon Manzon Allah. Ta yadda za mu mu'amalanci wawaye da hakurin Manzon Allah. Ta yadda za mu za mu fuskanci zalinci da adalcin Manzon Allah.

A haka Rabi'ul Awwal zai zo mana, ba wai wata a kalanda ba, sai a matsayin lokacin canja sabuwar rayuwa. A haifi halayenmu sababbi ta yadda za mu ji tamkar an haifemu tare da Manzon Allah (saw).

ALIYU DAHIRU ALIYU ✍️✍️✍️

Allah sarki, Masoyin Ruhi yana daf da zuwa,
23/07/2025

Allah sarki, Masoyin Ruhi yana daf da zuwa,

22/07/2025

Idan Matan hausawa da Fulani Basu godewa Allah ba, wallahi sun Banu 🤔🤔

MAIGIDA,KA ZAMA HASKEN ZUCIYAR MATARKA Aure  fa ba ciniki ba ne, ba Kuma dauri bane awuya ,shi alaka ce ta soyayya da ta...
08/07/2025

MAIGIDA,KA ZAMA HASKEN ZUCIYAR MATARKA

Aure fa ba ciniki ba ne, ba Kuma dauri bane awuya ,shi alaka ce ta soyayya da tausayi. Yana da matuƙar muhimmanci ga namiji ya fahimci cewa matarsa ba mai aikin gida ba ce kawai, ita wata abokiyar rayuwa ce da ta sadaukar da rayuwarta saboda kai kanka da iyalinka.

Ta bar gidan iyayenta ta biyo ka da don so da amana.

Tana jure wahala, ciwo, damuwa da gajiya domin ganin ka kasance cikin farin ciki.

Tana daukar nauyin tarbiyyar yaranku da kula da komai na cikin gida, ba tare da albashi ba, abunda take bukata kawai fatan kulawa da soyayya daga gare ka.

Don haka Ina kira ga mazaje:

Ku rika gaya masu kalmomin soyayya kamar irinsu "Na gode", "Ina alfahari da ke", "Allah ya saka miki da alheri". e.t.c

Ku tausaya musu idan basu da lafiya, ko sun gaji — ku taimaka musu, ku nuna musu damuwa.

Kada ku zamo masu tsauri ko fushi — ku zamo masu saukin fahimta da juriya.

Ka tuna da Annabi Muhammad(SAW ) ya kasance mafi kyawun miji, mai tausayi, mai wasa da iyalinsa, mai share hawayensu.

Mace na bukatar kulawa kamar yadda furanni ke bukatar ruwa. Idan ka kula da ita da tausayi da kalmomi masu daɗi, zaka girbi soyayya, kwanciyar hankali, da zaman lafiya a gidan ku.

Allah ya ƙara mana fahimta da zaman lafiya a cikin aurenmu.

Wani zaice shege don bashida matane kubarshi zaiyi ai!!😄😄

To Ina Addua

Nikuma Allah ya bani mata tagari 🤲🤲
Baffah Isa Bajoga ✍️

06/07/2025

Ka kalli zuciyarka kafin ka kalli lahirarka."
– Sheikh Tijjani (RA)

JUYAYI: SHAHADAR IMAM HUSSAINI (AS)JIKAN MANZON ALLAHﷺYau muna tuna daya daga cikin mafi girman ranaku na juyayi a tarih...
05/07/2025

JUYAYI: SHAHADAR IMAM HUSSAINI (AS)JIKAN MANZON ALLAHﷺ
Yau muna tuna daya daga cikin mafi girman ranaku na juyayi a tarihin Musulunci…

Shekara ta 61 bayan hijira… a cikin hamada da na filin Karbala…

Wani Matashi ne ya tsaya a gaban dubban makiya
Ba kisa, ba ƙarya, ba zalunci…
Sai dai gaskiya, adalci, da amana — irin wadda ya gada daga kakansa Manzon Allah ﷺ.

Imam Hussain (AS) – Jikan Annabi, Ɗan Sayyida Fatima (AS), ɗan Aliyu bn Abi Talib (AS)
Ya fuskanci mutuwa fiye da rayuwansa
Ya zaɓi shahada fiye da zalunci
Ya tsaya don kare dinin

Annabi Muhammadu SAWAW ❤️ 🙏 har da jinin jikinsa.

A Karbala, ba kawai Imam Hussain ne aka kashe ba. kafin kisan
An sare masa kai, an yanke masa hannaye, an kashe ‘ya’yansa da abokansa – har da yaro mai shayarwa – (Ali Asghar. AS)
An ƙone masa tantuna… an zubar da jinin Mai tsarki a kasa mai tsarki.

Amma duk da haka, bai taba rungumar zalunci ba.

Wannan shine Karbala.
Filin da ya dauki zafin gaskiya da ruwan jini.
Filin da hawaye ke gudu kamar ruwa a ido.
Filin da da'irar zalunci ta fadi, da ma'anar "Kada ka yarda da zalunci, ko da kuwa kana cikin ƙanƙanta" ta ɗaukaka.

Ya Allah, Ka saka da mafi alheri ga Imam Hussain da iyalansa, Ka haɗa mu da su a Aljanna, Ka hana mu daga cikin waɗanda s**a manta da Karbala.

Ya HUSSAIN.. Rayuwarka darasi ce. Mutuwarka sakon adalci ne har abada...

RANAR Ashura (10 ga watan Muharram), shekara ta 61 bayan hijira, wato 680 Miladiyya (CE) AKAYI YAKIN KARBALA
Baffah Isa Bajoga ✍️✍️✍️

30/06/2025

Har yau Banga Wanda Rakumi ya kawo Kara gurinsa ba Sai , Annabi Muhammadu SAWAW ❤️🙏

29/06/2025

Har yau Banga Wanda Zaki ya zaburo Kuma ya tareshi, Sai Annabi Muhammadu SAWAW ❤️🙏
Baffah Isa Bajoga ✍️

28/06/2025

Har yau Banga Wanda Rai yafita Amma ya Maida Ran
Sai Annabi Muhammadu SAWAW ❤️🙏
Baffah Isa Bajoga ✍️

Address

Unguwar Wakili Bajoga East, Funakaye LG
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Baffah Isa Bajoga posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share