MDwakili Ashaka

MDwakili Ashaka Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from MDwakili Ashaka, Baby & children's clothing store, Ashaka Cement Funakaye LGA, Gombe.

15/06/2026
YANZU-YANZU: Jam'iyyar APC Ta Ɗage Zaɓen Fidda Gwani Na ‘Yan Takarar Majalisar Wakilai Zuwa Ranar AsabarJam’iyyar All Pr...
15/05/2026

YANZU-YANZU: Jam'iyyar APC Ta Ɗage Zaɓen Fidda Gwani Na ‘Yan Takarar Majalisar Wakilai Zuwa Ranar Asabar

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da ɗage zaɓen fidda ‘yan takarar Majalisar Wakilai na babban zaɓen 2027 zuwa ranar Asabar, 16 ga Mayu, 2026.

Sanarwar ta fito ne cikin wata takarda da Kakakin Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Felix Morka, ya sanya wa hannu a Abuja ranar 14 ga Mayu, 2026.

Jam’iyyar ta bayyana cewa duk sauran ranakun da aka tsara domin gudanar da zaɓukan fidda ‘yan takara na sauran muƙamai ba su sauya ba.

Sabon jadawalin zaɓukan fidda ‘yan takarar APC ya kasance kamar haka:

Zaɓen Fidda ‘Yan Takarar Majalisar Wakilai — Asabar, 16 ga Mayu, 2026

Zaɓen Fidda ‘Yan Takarar Majalisar Dattawa — Litinin, 18 ga Mayu, 2026

Zaɓen Fidda ‘Yan Takarar Majalisar Dokokin Jihohi — Laraba, 20 ga Mayu, 2026

Zaɓen Fidda ‘Yan Takarar Gwamnoni — Alhamis, 21 ga Mayu, 2026

Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa — Asabar, 23 ga Mayu, 2026

APC ba ta bayyana takamaiman dalilin ɗage zaɓen na Majalisar Wakilai ba, sai dai masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin matakin na da alaƙa da shirye-shiryen cikin gida da kuma tabbatar da gudanar da zaɓukan cikin tsari da lumana.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci duk masu neman takara da magoya bayanta su ci gaba da bin dokoki da ƙa’idojin jam’iyyar yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓukan fidda gwani na 2027.

🌙📚 SUJUDA SAHW — YADDA AKE GYARA MANTUWA A SALLAH 📚🌙Mantuwa tana samun kowa…amma Musulunci ya koya mana yadda ake gyara ...
15/05/2026

🌙📚 SUJUDA SAHW — YADDA AKE GYARA MANTUWA A SALLAH 📚🌙

Mantuwa tana samun kowa…
amma Musulunci ya koya mana yadda ake gyara ta 🤲

📌 ABUBUWA 3 DA KE SA A YI SUJUDA SAHW:

1️⃣ RAGI (An-Naqs)
👉 Idan ka manta wani sunnah a sallah
(kamar tahiya ta farko)

2️⃣ ƘARI (Az-Ziyada)
👉 Idan ka ƙara wani abu a sallah
(kamar raka’a ta biyar ko ruku’u biyu)

3️⃣ SHAKKA (Ash-Shakk)
👉 Idan baka tabbatar raka’a nawa kayi ba

🌿 YADDA AKE YIN TA:

✅ KABLANI
(Sujuda kafin sallama)

👉 Ana yin ta idan an yi ragi a sallah.
👉 Za ka yi sujudu biyu kafin sallama.

✅ BA’ADI
(Sujuda bayan sallama)

👉 Ana yin ta idan an yi ƙari a sallah.
👉 Bayan sallama za ka sake yin sujudu biyu sannan ka yi sallama.

💡 Sanin wannan yana taimaka mana gyara sallarmu yadda ya dace 🌙

📌 Mantuwa tana samun kowa,
amma ilimi shi ne gyara.

💬 Ka yi Share domin wasu su amfana, kai ma ka samu lada 🤍

📲 Ku yi follow na wannan shafi domin samun fadakarwa, hadisai daga Manzon Allah ﷺ, da kuma amsoshin tambayoyinku cikin sauƙi.Naziru Bin Bashir

LABARIN SIYASA FUNAKAYE A yau ne ɗan takarar kujerar ɗan majalisar jihar mai wakiltar Funakaye North, Hon. Ibrahim Hamma...
03/05/2026

LABARIN SIYASA FUNAKAYE

A yau ne ɗan takarar kujerar ɗan majalisar jihar mai wakiltar Funakaye North, Hon. Ibrahim Hamma Ashaka, ya halarci ofishin jam’iyyar All Progressives Congress domin karɓar shaidar tsayawa takara a hukumance.

Hon. Ibrahim Hamma Ashaka tsohon ɗan siyasa ne wanda ya daɗe yana taka rawar gani a harkokin siyasa tare da bayar da gagarumar gudunmawa ga jam’iyyar APC da al’ummar mazabarsa.

Da yake jawabi bayan karɓar shaidar, ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa godiyarsa ga al’umma bisa irin kiraye-kirayen da s**a riƙa yi masa na ya fito ya tsaya takarar kujerar ɗan majalisar jihar domin wakiltar su. Ya bayyana cewa ya amsa wannan kira ne domin ci gaba da bautawa al’umma da tabbatar da ci gabansu.

Hon. Ibrahim Hamma Ashaka ya yi alƙawarin cewa idan aka ba shi dama, zai yi aiki tukuru wajen cika alkawurran da ya ɗauka, tare da tabbatar da cewa ba zai ba al’ummar Funakaye North kunya ba.

Haka kuma, ya buƙacih addu’o’in ‘yan uwa maza da mata, yana mai fatan Allah Ya tabbatar da nasara a wannan tafiya tare da ba shi ikon sauke nauyin da al’umma s**a ɗora masa.

Al’ummar Jihar Gombe sun nuna cikakkiyar amincewa da goyon baya ga Sanata Sa’idu Ahmad Alkali, bisa la’akari da nagartar...
11/04/2026

Al’ummar Jihar Gombe sun nuna cikakkiyar amincewa da goyon baya ga Sanata Sa’idu Ahmad Alkali, bisa la’akari da nagartarsa, gaskiyarsa da kuma kishinsa ga cigaban jihar.
Sanata Sa’idu Ahmad Alkali mutum ne da ya dade yana hidimtawa al’umma da zuciya daya, yana kokarin kawo sauyi mai ma’ana da kuma inganta rayuwar jama’a. Tarihinsa na shugabanci ya nuna cewa shi mutum ne mai hangen nesa, wanda ke da kudurin kawo ci gaba a fannoni daban, daban.
A wannan lokaci da al’ummar Jihar Gombe ke bukatar shugaba mai tausayi, hikima da jajircewa, babu shakka Sanata Sa’idu Ahmad Alkali ya dace da wannan nauyi. Tsayawarsa takarar gwamna wata dama ce ta ceto al’umma daga matsaloli tare da gina makoma mai kyau ga kowa.
Muna kira ga daukacin al’umma da su ci gaba da nuna goyon bayansu cikin lumana da mutunta juna, domin hadin kai shi ne ginshikin samun nasara. Mu hada hannu wajen tabbatar da shugabanci nagari da zai kawo ci gaba, zaman lafiya da walwala ga Jihar Gombe.
Allah Ya tabbatar da alheri, Ya ba mu shugabanci nagari.

DAN ALKALI AGAIN
ZINARIYAR FUNAKAYE SOCIAL MEDIA ✍🏿

10/04/2026

With Mu'assasatu Sheikh Muhammad Rabi'u Litahfizul Qur'an – I just got recognized as one of their top fans!

Address

Ashaka Cement Funakaye LGA
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MDwakili Ashaka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share