AH KURA & Associates

AH KURA & Associates Architect designing

18/01/2016
12/07/2015

FA'IDODIN DA SUKE CIKIN YIN AURE
*************************************
Fa'idodin da suke cikin aure ba zasu Kididdigu ba. Amma ga wasu ka'dan daga ciki zamu lissafo kamar haka:

1. Yin aure biyayya ne ga Umurnin Allah da Manzonsa.

2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (S.A.W) farin ciki aranar lahira. Yace : "Kuyi aure ku hayayyafa. Domin ni zanyi ma sauran al'ummomi alfahari daku aranar Alkiyamah".

3. Ta dalilin aure zaka samu wanda Zai fito ta jikinka, har ya girma yana Kalmar Shahada!! "LA ILAHA ILLAL LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI".

4. Ta dalilin aure ne zaka samu Zuriyar da zasu yi maka addu'a bayan rasuwarka. Wannan yana daga cikin ayyukan da ladansu ba zai yanke ba har abada.

5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun mutum daga kalle kallen Haramun, sannan ya kare masa al'aurarsa daga Zina.

6. Ta dalilin aure ne zaka samu damar taimaka ma 'Yar uwarka Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta kenan daga Zina.

7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar addininka, da ninkawar ladanka fiye da wanda basu da aure.

8. Ta dalilin aure ne zaka samu ladan ciyarwa da Matarka, da daukar nauyinta, da ladan samar mata da Mazaunin da zata rayu.

9. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Qara yawan Musulman duniya ta hanyar haihuwar da zaka samu.

10. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Karkatar da himmarka daga kan neman biyan bukatarka ta hanyar haram izuwa ga hanyar halal. Da kuma samun ladan saduwa da iyalanka.

11. Zaka samu lada mai girma sosai idan Har Allah ya azurtaka da 'Ya'ya mata guda biyu, kuma kayi hakuri dasu ka kyautata musu, ka kyautata tarbiyyarsu, Su zasu zama Garkuwarka daga shiga wuta.

12. Idan har 'Ya'yanka guda biyu s**a rasu, kuma kayi hakuri, to Allah zai shigar dakai Aljannah saboda wannan.

13. Ta dalilin aure zaka samu Qaruwar mutuncinka da darajarka acikin al'ummah. Ka shiga sahun mutanen da zasu iya jagorantar lamuran rayuwar al'ummah.

14. Ta dalilin aure ne zaka Samu Taimakon Allah cikin al'amarinka. Kamar yadda Manzon Allah (saww) yake cew

04/06/2015

MAZAN NE KO MATAN NE.?
1. Ina mamakin wai ko wanne namiji idan ya
tashi yin aure wai FARAR MACE yakeso mai kyau
malam kai FARI ne ko KYAWUN ne da kai.???
2. Idan da ace MATA zasu cire son kudi da abin
duniya suma s**e sai fari dogo mai hanci mai
kyau sukeso su aura, don Allah MAZA nawa ne
kenan zamu AURU 5% ko 10%
3. Sannan sai kaga namiji ya dage wai shi sai yar
mai KUDI zai aura tokai dan mai KUDI ne.???
4. Kema MACE ki dage waike sai mai kudi zaki
aura, to a lokacin da mahaifinki yayi auren farare
bugun Abuja nawa yake dasu.???
5. Sai kaga namiji ya dage waishi ba zaiyi aure
ba sai yayi KUDI, tambayata a nan shine kasan
lokacin da zakayi KUDIN,??? Kuma nawa ne zaka
mallaka a duniya.???
6. Haba yan MATA wai kema sai ki dage lallai sai
anyi miki LEFE akwati 12 wata ma sai dai 14, yan
MATA koma gida ki tambayi mahaifiyarki akwati
nawa ya kawo tsohonki ya kawo mata a lokacin
da zai aureta,??? Wata kila ma KWALLA ce 1 ko
2.
7. Yan MATA kun jefa SAMARI akan sai sunyi
kudi ta ko wanne hali sannan zaku auresu, wanda
ta hakan wasu sun koma 419, wasu sata kawai
don su auri FARAREN MATA masu kyau.
8. mu kuma MAZA mun jefa MATA a Bala'I na
BLEACHING, SHIGAR BANZA, NUNA TSARAICI,
BARA'A GA DOKAN ALLAH, kawai don su auri
namiji mai kudi mai kyau
9. SAMARI da yan MATA mu ajiye burukan dake
makare a cikin zucuyoyin mu, mu rufawa juna
asiri
10. MAZA da MATA mu farga wallahi ba haka
iyayen mu s**a rayu ba, kuma zanyi muku
gargadi mafi tsoratarwa dan duk wanda ya kuma
takurawa MATA ni dashi ne.

01/06/2015

Allah katsaremu dagayin bidi'a amin

23/04/2015

slm jama.ar musulmi ina muku barka da dare

Address

No R10 Atiku Auwal Road Opposite Danfodio Mosque Unguwar Sanusi Kaduna
Kaduna South

Telephone

+2347036154454

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AH KURA & Associates posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share