09/11/2025
Ka Taɓa Samun Wannan Matsalar A P2P? Ga Yadda Zaka Magance ta.
Ka taɓa zuwa P2P zaka siya dollar bayan ka tura kuɗi wa merchant sai botton ɗin da zaka danna 'Mark as paid' ma'anar ka tura kuɗi yaƙi dannuwa har order ɗin tayi cancel? Kuɗin ka suna hannun merchant, kuma order tayi cancel, kana tayiwa merchant ɗin magana baya kula ka ko yaƙi dawo maka da kuɗin ka?
✅ Abinda zakayi shine idan order ɗin tayi cancel, kaje wajen list ɗin merchants da suke P2P, ka duba wannan merchant ɗin, saika sake saka order ta BUY, ta daidai adadin daka siya. Idan N50,000 ka tura masa, ka sake saka order ta same N50,000. Karka ƙara ko ka rage, sai kaje kayi chat dashi, zai baka amsa, idan bai baka ba, sai ku tafi appeal. Kayi musu bayani, basu fiya bari aje appeal ba idan hakan ya faru. In shaa Allahu zai sakar maka USDT ɗin ka.
✅ Ku kiyaye, saboda kar hakan yake faruwa daku, sai kun fara danna kun turawa merchant kuɗi kafin ku tura musu da kuɗi, musamman idan kuɗin da yawa, saboda gudun samun irin wannan matsalar. Ba haka Exchanges s**a tsara ba, amma saboda gudun samun matsala gwara kayi haka, in yaso in kuɗin bai turu ba, ko wata matsalar ta samu, sai kayi cancel na order ɗin.
✅ A ƙarshe, a daina son arha ko sauki ake yin P2P da verified merchant, yana rage maka risk ɗin samun matsala a P2P da percentage mai yawa.
GM