Duniyarmu A Yau

Duniyarmu A Yau shafine Wanda zai dinga kawo muku abinda yake faruwa a duniya Baki daya muna muku barka da shigowa shafinmu na Hausa Novels

UWAR MUGU-01Daga Littattafan Nazir Adam Salih.*KIBIYAR AJALI**ME YAFI KUDI**TA LEKO TA KOMA**BIRNIN SARAUNIYA**MUTUWAR K...
22/08/2026

UWAR MUGU-01

Daga Littattafan Nazir Adam Salih.

*KIBIYAR AJALI*
*ME YAFI KUDI*
*TA LEKO TA KOMA*
*BIRNIN SARAUNIYA*
*MUTUWAR KASKO*
*NAIRA DA KWABO*
*ACI BULUS*
*ALAKAKAI*
*WA NA K**A*
*HINDU*
*RUHINA*
*DARE DA RANA*
*KARYA LINZAMIN SHAIDAN*
*CUTA TA DAU CUTA*
*ISKA MAI KADA RUWA*
*BINDIGAR KWALI*
*DAMISAR TAKARDA*
*AZIZA*
*TSOHON ALKAWARI*
*KAI DA JINI*
*ALJANI YA TAKA WUTA*
*KUDI DA MACIJI*
*KISAN BOKO*
*KURA DA KAN RAGO*
*MURMUSHIN ALKAWARI*
*ZAYYANA*
*ZABIYA*
*MUGUN JI*

DON ABOKINA
Engr Auwal Sani Kabo.

UWAR MUGU
Copyright © Nazir Adam Salih 2010
Hakkin Mallaka (h) Nazir Adam Salih 2010

TARIHIN DABA'INSA
An fara Buga shi a Kamnas Publishers Dakata
Kano A shekarar 2010

GARGADI
Ba'a yarda wata kungiya ba ko wani mutum ya juya wani bangare na wannan littafin ta hanyar wasan kwaikwayo da majigi ko kuma wani abu daban saida tabbataccen izinin marubucin.

ADIRESHI
Abubakar Saddik Islamiyya Dakata Kano.
Akwatin Gidan Waya 4792.

UWAR MUGU
Nazir Adam Salih
(Nas)

BABI NA DAYA
ALIYA na zukar sigarin dake hannunta saita dafe makogoro cikin kaduwa sannan tafara tari kufur kufur nan da nan jikinta ya dauki rawa. Cikin sauri ta fice daga da'irar yan matan dake gaban makadin takoma can gefe guda sannan tafara nazarin su daya bayan daya tana mai addu'ar Allah yasa dai babu wanda ya lura da ita ballantana ma har ace tayi abin kunya ita dai ta sha fadi cikin zuciyarta cewa wannan abu ba dadinsa take ji ba mutum yayi ta hurawa cikinsa hayaƙi makoshinsa ya shake k**ar zaka mutu amma don masifa sai an sha tunda yazama al'adar duk wata karuwa dake gurin abin kunya ne a ganki ma baki iya busa hayaƙi sama ba don haka wannan gudun abin kunyar shiyasa Aliya tafara busa hayaƙi sama amma ba wai don tana so ba.

Aliya ta tofar da yawu sannan tayi jifa da guntuwar tabar dake hannunta gamida ajiyar zuciya daga inda take tsaye tana iya hangen samari da yan mata dakuma dattijai masu budurwar zuciya sunata cashewa agaban DAN INDO wani dattijo dan duniya sanye da katon wando buje da dogon gemu k**ar saman jinka ga tarin gashin baki k**ar ciyawa yana tsakiya da mataji a hannunsa ana kida yana rawa lokaci guda kuma yana taje gemunsa da matajin yan duniya na ta watsi da Nairori a kansa kai ka rantse da Allah babu sauran talauci acikin kasa.

Mafi yawan daga cikin matan sanye suke da kaya iri daya sunyi Asin-da-Asin musamman don wannan ajo na FATI ZAFI ZAFI yan tsirarin karuwai masu rangwamen gata da wadanda ta karewa sune kawai s**a fita zakka a cikinsu harda Aliya duk kuwa da cewa tafi duk wata karuwa dake gurin kyawun sura nesa ba kusa ba amma halayyar na tayi-da-fasawa ita ta ja mata shiga halin bakin talauci a halin yanzu talaucin daya hana mata ankon ajon kawarsu fati zafi-zafi.

Aliya ta dubi agogon kan fuskar wayar dake hannunta karfe biyu saura na dare. Adaidai lokacin ne dan indo yafara hada kayansa da komotsansa yan duniya s**a fara k**a gabansu suna shiga cikin garin TAFA domin cigaba da cin kasuwar dare.

Wannan shagali anyi shine cikin wani katon fili na wasan kwallo kafa dake bayan garin Tafa. Tun farko ita fati zafi zafi wadda ta shirya bikin ajon domin tara masu gidan rana bahaka taso ba taso ne ace acikin farfajiyar wata kayatacciyar otal aka yi bikin to amma sa'ar data lalubi aljihunta taji babu tudu saita ga batada zabi illa ta tara mutane a cikin katon filin a cashe akalla dai tayi imani ko mai zaije yadawo sai ta sami RIBA.

Daga filin kwallon kafan idan ka dubi bangaren kudu babu komai sai tarin bishiyoyi da kuma ciyayi gamida wani tsohon gidan mai wanda ya jima a rufe ba'a sayar da komai acikinsa sai beraye ne ke ta gada aciki.

Adab da inda wannan gidan mai a tsugunne yayi tagumi sanye d kaya dukun dukun k**ar anyi barin mota dashi wani saurayi ne ya zurawa dandalin bikin idanu yana kallon jifa jifan mata da maza nan da can ana ta hira ana karawa sararin samaniya hazo.

Wannan saurayi yafi sa'o'i shida zaune agurin yayi zuru k**ar mujiya yana kallon duk shagalin dake faruwa agurin dayawa daga cikin yan duniyar dake kai kawo a filin sun dauke shi ne amatsayin tababbe.

Tsakanin inda saurayin dake tsugunne zuwa inda Aliya take tsaye baifi taku goma ba.
Aliya ta dubi saurayin dake tsugunne agurin kana ta dauke kai cikin tausayi a zuciyar ta tana cewa.
Mutane dai basuda kirki gashi dai kyakkyawa da kuruciyarsa amma sai da aka samu wani marar imani ya haukata shi Aliya tayiwa kanta murmushi adaidai lokacin da wasu kawayen ta s**a nufo inda take ta sake duban saurayin ta dauke kai.
Yanzu haka shaye shaye ne tace da kanta adaidai lokacin da su LARABA s**a karaso inda take.

Laraba na karasowa saita dubi Aliya a yatsine
Kedai wallahi kinji kunya Shikenan don kawai bakiyi dinkin anko ba sai ki wani koma gefe k**ar wata marainiya?

Aliya ta Harare ta.
Ke banza bakya ganin gurin ya cushe da kyar ake numfashi shiyasa na koma gefe na sha iska.

ASABE ta fashe da dariya shegiya Aliya akwai ki da iya kwana k**ar mota to meye in baki yi anko ba akanki aka fara?

Aliya ta tafa hannu tace oh Ni Aliya na shiga uku to wai ina ruwan ku ne? Zan fa ci uban yarinya Wallahi ta dube su a fusace.

Laraba ta fashe da dariya Haba ƙawata ke baki san wasa bane?

Toh Ai ku ne da abin haushi Aliya tace sannan ta sake duban agogon dake wayarta

Laraba ta turo dankwalin ta gaban goshi sannan ta lalubi aljihu jakarta ta dauko karan taba ta cinna masa wuta ta busa hayakin sama kana ta dubi Aliya tace.

Kai gaskiya zafi zafi ta sami kudi yau anya kuwa ni ma ba ajon nan zan shirya ba.?

Kin rigani afili na riga ki a zuciya kinga yanda shegen nan alhaji DAN ABU yayi ta lika mata yan dubu dubu? Yafa taba nemana amma saboda yanzu yaga sabuwar fuska sabon jini ko kallo ban ishe shi ba. Asabe tace tana zazzare idanu.
Laraba ta Busa hayaƙi sama tabi shi da kallo.

Kedai abar tone tone kawai Amma in wannan ne Nima yataba nemana kuma har......
By Jikan sidi me jaka

22/08/2026

BARKANKU DA WANNAN LOKACI

Wannan shafi me albarka Yana farincikin sanar daku cewa zamu fara kawo muku littattafan Hausa ,Wanda zasu saku nishadi ,bandariya,ban al'ajabi,har ma da ban haushi

Muna fata zaku bamu hadin Kai ta hanyar yi mana liking akan post da comment

Mun gode
✍️By duniyarmu A Yau

Address

Zaria Road Rigasa Kaduna
Kaduna
800001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniyarmu A Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Duniyarmu A Yau:

Shortcuts

Share