14/04/2026
SAURAYINKI NA TAƁA JIKINKI… KUMA KICE KIN SAMU MIJI? UBAN YAYA FASIQI MARA TSORON ALLAH''
Ya ke ‘yar uwa… ki tsaya ki saurara da zuciya 💭
Wanda bai girmama ki ba kafin aure…
Yaya k**e tunanin zai girmama ki bayan aure? 😔
💔 Saurayin da:
👉 Yake taɓa jikinki ba tare da kunya ba
👉 Yake wuce iyakar da bai kamata ba
👉 Yake ja ki zuwa abin da bai dace ba
❗ Wannan ba miji nagari bane… fasiki ne mara tsoron Allah.
⚠️ Ki sani:
Namiji mai tsoron Allah yana kare mutuncinki… ba zai lalata shi ba.
😢 Idan yau:
– Baya jin kunyar fasikanci
– Baya girmama iyaka
– Baya kula da addini
👉 Me zai hana gobe ya cigaba da neman wasu mata ko bayan ya aure ki?
💡 Ki tambayi kanki:
❓ Shin wannan soyayya tana kai ni ga alkhairi ne ko halaka?
❓ Shin yana kare mutuncina ko yana lalata shi?
🌿 Ki sani:
✔️ Miji nagari yana jira halal
✔️ Miji nagari yana girmama ki
✔️ Miji nagari baya matsa miki zuwa haram
💔 Wasu mata sun yarda…
S**a ba da jikinsu…
A ƙarshe kuma aka bar su aka tafi 😢
⚠️ Kada ki:
– Yaudare kanki da kalmar “zan aura ki”
– Rasa mutuncinki saboda soyayya
– Amincewa da wanda baya tsoron Allah
🌸 A ƙarshe:
Ki tsare kanki… ki tsare mutuncinki…
Domin wanda ya lalata ki kafin aure, ba zai daraja ki bayan aure ba.
🤍 Idan wannan ya taɓa zuciyarki… ki tura wa wata ‘yar uwa. Kumin shearing kawai
Allah ya kiyaye mu daga kuskure 🤲
✍️ Dr Ibrahim Hudu Marubuci