29/06/2026
ZA A GINA SECURITY PLAZA A GADAR ƊAN’AGUNDI DA GADAR TAL’UDU, TARE DA SANYA NA’URORIN CCTV A GADAR ƊAN’AGUNDI DOMIN ƘARA INGANTA TSARO.
— Kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Engr. Marwan Ahmed Aminu.
Rahoto daga: Khamis Bashir Bako Ayagi, mai ɗauko wa Gwamna rahoto a Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kano.
Alhamdulillah! Yayin da gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Engr. Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) ke ci gaba da kammala manyan ayyukan more rayuwa da ta fara, yanzu haka ta ɗauki wani muhimmin mataki na tabbatar da cewa waɗannan ayyuka sun samu cikakken tsarin tsaro da kariya.
Da yake bayyana hakan, Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Engr. Marwan Ahmed Aminu, ya ce bayan kammala aikin gina Gadar Ɗan’Agundi da Gadar Tal’udu, gwamnatin jihar ta ba da umarnin gina Security Plaza a waɗannan gadoji domin samar da ingantaccen tsaro ga masu amfani da su da kuma kare muhimman kadarorin gwamnati.
Ya ƙara da cewa, Security Plaza ɗin ba zai kasance gini kawai ba, zai kasance cibiyar gudanar da ayyukan tsaro, inda za a jibge jami’ai daga hukumomi daban-daban domin aiki tare a ƙarƙashin tsari guda.
Jami’an da za su kasance a waɗannan cibiyoyin sun haɗa da:
Jami’an Yan Sanda, NSCDC (Civil Defence), KAROTA, Hisbah, Yan Kato da Gora (Vigilante), jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), da sauran hukumomin tsaro da s**a dace.
Baya ga haka, Kwamishinan ya bayyana cewa za a sanya na’urorin sa ido na CCTV a Gadar Ɗan’Agundi domin lura da duk wani motsi a kowane lokaci, da kuma taimakawa jami’an tsaro wajen hana aikata laifuka, gaggauta kai ɗauki idan buƙata ta taso, da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Wannan wani ƙarin tabbaci ne cewa gwamnatin jihar Kano ba wai tana gina tituna da gadoji kaɗai ba ne, tana gina tsarin da zai tabbatar da dorewar waɗannan ayyuka, kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da samar da ingantaccen yanayin zirga-zirga ga kowa.
–Khamis Bashir Bako Ayagi
SR – Ministry of Works, KNSG
29/06/2026