31/08/2026
TATTAUNAWA AKAN KALUBALEN DA KASUWAMCI KE CIKI A AREWACIN NIGERIA TARE DA KARRAMA ZABEBBEN SHUGABA ALH. MUSA NABANKI.
Shugaban Kasuwar Singer da Kewaye, Alh. Musa Ibrahim Nabanki ya jagoranci wani taro mai muhinmanci akan tabarbarewar Kasuwaci da Kuma halin da Yan Kasuwa suke ciki a Arewacin Nigeria...
Taron wanda ya hada Yan Kasuwa daga bangarori daban daban na Arewacin Nigeria ya tattauna hanyiyin da za'abi tare da bawa Gomnatoci daga kowanne mataki shawarwarin hanyoyin da ya k**ata abi matukar anaso kasuwacin Arewacin Nigeria ya farfado a kasar ma baki daya.
Shugabannin Yan Kasuwa daga jahohi da dama sunyi tsokaci da tare da fito da hanyoyin da ya k**ata Yan Kasuwa daga kowanne mataki ya k**ata sudinga dauka idan sun fada cikin wani hali yayin da jarinsu ya ragu ko kuma wani sabon yanayi da suke shiga duk lokacin da s**a fada cikin wani hali na koma bayan jarinsu.
Daga karshe kungiyoyi daban daban sun girmama Shugaban Kasuwar ta Singer da lambobin yabo bisa jajircewarsa da hidintawa Jama'a Musanman kananu da manyan Yan Kasuwa dake fadin jihar kano da Arewacin Nigeria baki daya.