03/05/2026
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu, ya ku al’ummar Karamar Hukumar Malumfashi.
A yau ina tsaye a gabanku a matsayin É—a na gari mai alfahari, matashi É—an Najeriya mai cikakken imani da makomar jiharmu, domin bayyana burina na tsayawa takarar zama Memba na Majalisar Dokokin Jihar Katsina, mai wakiltar mazabar Malumfashi.
Ni matashi ne, amma ba bakon wahalhalun da al’ummarmu ke fuskanta ba ne. Na taso ina gani da ido irin ƙalubalen da iyalanmu ke fuskanta daga rashin aikin yi ga matasa, ƙarancin samun ingantaccen ilimi, rashin wadataccen kiwon lafiya, har zuwa lalacewar ababen more rayuwa. Saboda haka na zaɓi tafarkin hidima mai ma’ana maimakon zama ina kallo ko koke kawai.
Na yi imani cewa matsalolin zamani na bukatar hanyoyin magance su na zamani, kuma dole ne a ba matasa dama su kawo kuzari, kirkira da sabbin dabaru a shugabanci.
Ba na roƙon wannan dama a matsayin alfarma ba; ina nema ne a matsayin haƙƙi da kuma buƙata domin ci gaba mai dorewa.
Ban zo da alkawura marasa tushe ba, sai dai da tsari mai kyau, manufofi, da ƙuduri mai ƙarfi na yi wa jama’a hidima.
Haka kuma, Zan tabbatar da gudanar da tarukan tattaunawa da jama’a a kai a kai wato Town Hall meetings, gabatar da rahoton aiki duk bayan watanni uku ga mazabata, da kuma buɗaɗɗen ofishi ga kowa. Wakilcina zai kasance bisa kusanci da jama’a, sauraron koke kokensu, da kuma samar da sakamako mai ma’ana.
Ga ’yan uwana matasa: Wannan shi ne lokacinmu. Mu guji zama masu sakaci, mu shiga siyasa da himma. Canjin da muke nema ba zai zo daga gefe ba, sai mun shiga tsakani da hannu biyu. Ina kira ga matasa, mata, dattawa, ƙwararru, ’yan kasuwa, masu sana’o’i, da dukkan masu kishin al’umma da su zo mu haɗa kai domin gina Malumfashi mafi alheri.
Ina roƙon goyon bayanku cikin tawali’u addu’o’inku, shawarwarinku, da mafi muhimmanci ƙuri’unku a zaɓukan fidda gwani da babban zaɓe mai zuwa. Tare za mu tabbatar cewa jagorancin matasa ba haɗari ba ne, a’a shi ne mafi kyawun jari ga makomar mu baki ɗaya.
Allah Ya albarkace ku. Allah Ya albarkaci Malumfashi. Allah Ya albarkaci Jihar Katsina.
Naku
Muhammad Sadi , MSJ
Wazirin Sarkin adon galadiman katsina