AURE Sunnah

AURE Sunnah Good behaviors

KAFIN KA AURI MACE, KA BINCIKI WAƊANNAN ABUBUWA 5 GAME DA IYAYENTA.​Ɗan uwa, kashi 98% na mata suna tafiyar da rayuwar a...
31/07/2026

KAFIN KA AURI MACE, KA BINCIKI WAƊANNAN ABUBUWA 5 GAME DA IYAYENTA.

​Ɗan uwa, kashi 98% na mata suna tafiyar da rayuwar aurensu ne daidai yadda s**a ga ana yi a gidansu. Wannan gaskiya ce wadda babu wata soyayya da za ta iya canza ta. Yarinya ba za ta taɓa ba ka abin da ba ta gani an yi a gidansu ba.

​Kafin ka ɗauko wutar daji ka kawo ta gidanka, tabbatar ka yi bincike akan waɗannan abubuwan guda 5:

​1. Addinin Iyayenta Da Irin Tarbiyyar Su:
Idan iyayenta ba su da kyakkyawan riƙo da addini ko sanin ya kamata, akwai babban aiki a gabanka. Tarbiyyar gida ita ce asali. Mace mai tsoron Allah daga gidan masu tsoron Allah take fitowa.

​2. Yadda Suke Gudanar Da Zaman Aurensu:
Idan a gidansu uwa ce take juya gida, ko raina miji ruwan dare ne, ka tabbata yarinyar nan haka za ta yi maka. Yarinya tana koyon biyayya da girmama namiji ne kai tsaye daga wajen mahaifiyarta.

​3. Yadda Suke Warware Saɓani
Idan faɗa ya tashi a tsakanin iyayenta, yaya suke warwarewa? Idan zagi ne, ɗaga murya, duka, ko tona asirin juna a waje, ka sani cewa wannan ita ce dabi'ar da za ta ɗauko idan kun samu saɓani a gidanka.

​4. Yadda Suke Girmama Zumunci Da Na Gaba:
Binciki yadda gidansu suke karɓar baƙi, riƙe 'yan uwa, da girmama na gaba da su. Idan gidansu ba a daraja ɗan uwa kuma babu tsarin karrama mutane, za ta wargaza taka dangin ne idan ka kawo ta.

​5. Tarihin Kwaɗayi Ko Rufin Asiri
Shin iyayenta masu rufin asiri ne da godiyar Allah, ko masu kwaɗayi da nuna bura-uba? Idan ta taso a gidan da ake auna mutuncin ɗa namiji da girmansa ta hanyar kuɗin da yake da shi kawai, ba za ta taɓa gamsuwa da ɗan abin da kake da shi ba a lokacin da arziƙi ya yi ƙasa.

​Aure ba soyayyar fuska ko kyan sura ba ne kawai; haɗa jini ne da asali. Idan asalin ya ɓaci, kai ne za ka sha wahalar gyarawa, har ma abin ya shafe makomar 'ya'yanka.
​UMAR ALIYU DAHIRU ✍️

Address

Unguwan Sarki
Lere

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AURE Sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share