The Secretary Zaria LG

The Secretary Zaria LG This is the official page of the Office of the Council Secretary, Zaria Local Government

15/06/2026

Permit me to borrow the popular slogan, “KOWA NAMU NE”

Uba Sani 2 times✌️

Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), ya karbi wata kungiyar goyon baya da aka kafa kark...
15/06/2026

Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), ya karbi wata kungiyar goyon baya da aka kafa karkashin jagorancin Dujiman Kaita, Amb. Abubakar Tahir Abubakar, domin dawowar Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Senator Uba Sani, da Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Abbas Tajudeen, tare da dukkan ‘yan APC a Zaria da ma Jihar Kaduna baki daya. Wannan na daga cikin kokaarin ci gaba da tabbatar da kyakkyawan shugabanci da cigaban Karamar Hukumar Zaria karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga).

A yayin ziyarar da kungiyar ta kawo, Sakataren ya yi musu maraba tare da jaddada shirye-shiryen karamar hukumar na yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki na gaskiya wadanda ke da burin inganta shugabanci da ci gaban Zaria.

A wani bangare na ziyarce-ziyarcen da aka kawo mai, Sakataren ya kuma karbar shugabannin APC na Mazabar Gyellesu karkashin jagorancin Shugaban Mazabar, Mallam Isma’ila Mainasara (Mai Shinkafa). Tawagar ta kai ziyarar girmamawa ga Sakatariyar Karamar Hukumar bayan sun gudanar da zagayen duba ayyuka da dama na ci gaba da Gwamna Uba Sani da Rt. Hon. Dr. Abbas Tajudeen s**a aiwatar a Zaria, musamman a Gyellesu.

Sakataren ya yaba wa shugabannin bisa jajircewarsu wajen hidimtawa jam’iyya, tare da karfafa musu gwiwa da su kara himma wajen wayar da kan jama’a, ta hanyar bayyana manyan ayyuka masu da gwamnatin APC ta aiwatar, maimakon dogaro da tallafi na wucin gadi kawai.

Domin nuna goyon baya da karfafa guiwa ga shugabannin, Sakataren ya ba su gudummawar Naira Dubu Dari (N100,000) domin tallafa wa ayyukansu na jam’iyya da ci gaban harkokin siyasa a matakin kasa.

Shugabannin KPC Support Group Zone 1, tare da coordinators na kananan hukumomi takwas da ke Zone One, sun kawo ziyara ga...
15/06/2026

Shugabannin KPC Support Group Zone 1, tare da coordinators na kananan hukumomi takwas da ke Zone One, sun kawo ziyara ga Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), wanda ya karbe su yayin da yake wakiltar Shugaban Karamar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga).

A yayin ziyarar, tawagar ta gabatar da manufofin kungiyar na siyasa da tsare-tsaren wayar da kan jama’a da neman goyon baya daga matakin kasa, tare da neman shawarwari kan yadda za a inganta tsari da shugabanci domin karfafa tafiyar kungiyar a fadin Zone 1.

Saboda irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban siyasa da kuma jagoranci na gari, kungiyar ta sanar da nada Sakataren a matsayin Uban kungiyar. Haka kuma, a wannan ziyara ne aka kaddamar da kungiyar a hukumance, inda Sakataren ya mika takardun nadi ga sabbin shugabanni.

A jawabansu, shugabannin kungiyar sun sake jaddada cikakken goyon bayansu ga sake zaben Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Senator Uba Sani, da Abbas Tajudeen, tare da dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC a Zone 1 da kuma Jihar Kaduna baki daya. Sun kuma yi allawarin yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabubuka masu zuwa.

A matsayin nuna goyon baya da karfafawa ga kungiyar, Sakataren ya tallafa wa tawagar da kudi har Naira 50,000 domin taimakawa wajen harkokin sufuri na mahalarta taron. Wannan karamci ya samu yabo da godiya daga shugabannin kungiyar da mambobinta.

HAPPY DEMOCRACY DAY!Fellow Citizens of Zaria Local Government,As we celebrate this year's Democracy Day, let us honour t...
12/06/2026

HAPPY DEMOCRACY DAY!

Fellow Citizens of Zaria Local Government,

As we celebrate this year's Democracy Day, let us honour the heroes of our past who fought for our freedom and the democratic values we enjoy today.
Democracy is not just about elections; it is about good governance, accountability, justice, and the active participation of every citizen in building a better society.

Let us continue to promote peace, unity, tolerance, and respect for the rule of law as we work together for the progress and development of Zaria Local Government and Nigeria at large.

On behalf of the Local Government Council and the good people of Zaria, I wish you all a peaceful and joyful Democracy Day celebration.

Long live democracy, Long live Nigeria!

11/06/2026

Yesterday homage visit to Sarkin Zazzau, Amb. Ahmad Nuhu Bamalli, CFR.

Allah ya kara ma Sarki lafiya.

𝐒𝐀𝐊𝐀𝐓𝐀𝐑𝐄𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐀𝐌𝐀𝐑 𝐇𝐔𝐊𝐔𝐌𝐀𝐑 𝐙𝐀𝐑𝐈𝐀 𝐙𝐀𝐑𝐈𝐀 𝐘𝐀 𝐊𝐀𝐑𝐁𝐈 𝐁𝐀𝐊𝐔𝐍𝐂𝐈𝐍 𝐙𝐀𝐒𝐌𝐎 𝐃𝐀 𝐀𝐋-𝐐𝐈𝐁𝐋𝐀 𝐂𝐇𝐀𝐑𝐈𝐓𝐘 𝐅𝐎𝐔𝐍𝐃𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍, 𝐘𝐀 𝐁𝐀𝐘𝐀𝐑 𝐃𝐀 𝐍𝟏𝟓𝟎,𝟎𝟎𝟎Sakata...
10/06/2026

𝐒𝐀𝐊𝐀𝐓𝐀𝐑𝐄𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐀𝐌𝐀𝐑 𝐇𝐔𝐊𝐔𝐌𝐀𝐑 𝐙𝐀𝐑𝐈𝐀 𝐙𝐀𝐑𝐈𝐀 𝐘𝐀 𝐊𝐀𝐑𝐁𝐈 𝐁𝐀𝐊𝐔𝐍𝐂𝐈𝐍 𝐙𝐀𝐒𝐌𝐎 𝐃𝐀 𝐀𝐋-𝐐𝐈𝐁𝐋𝐀 𝐂𝐇𝐀𝐑𝐈𝐓𝐘 𝐅𝐎𝐔𝐍𝐃𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍, 𝐘𝐀 𝐁𝐀𝐘𝐀𝐑 𝐃𝐀 𝐍𝟏𝟓𝟎,𝟎𝟎𝟎

Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar Zaria, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya karbi bakuncin wasu mutane, kungiyoyi da gidauniyoyi daban-daban a ofishinsa.

Daga cikin fitattun kungiyoyin da s**a ziyarce shi akwai ZARIA APC SMART MOVEMENT (ZASMO), wata kungiya domin wayar da kan jama’a da tattara goyon baya domin sake zaben Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Senator Uba Sani, Rt. Hon. Abbas Tajudeen da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC a Zaria.

Sakataren, wanda yake daya daga cikin masu ruwa da tsakin kungiyar, ya yaba da kokarin da suke yi wajen karfafa jam’iyyar APC a Zaria tare da tabbatar musu da cikakken goyon bayansa. A karshen ganawar, ya ba kngiyar tallafin kudi Naira 50,000 domin saukaka musu harkokin zirga-zirga.

Haka kuma, Sakataren Majalisar ya karbi bakuncin ZARIA AL-QIBLA CHARITY FOUNDATION, wata kungiya mai karfi da ta hada fiye da kungiyoyin mata 20 a fadin Zaria. Tawagar ta kai ziyarar ne domin nuna godiya bisa gudunmawar da ya bayar wajen samar musu da dakin taro na Sakatariyar wanda ya taimaka wajen gudanar da shirinsu cikin nasara.

Da yake yaba da ayyukan jin kai da karfafa mata da kungiyar ke yi, Sakataren ya tallafa musu da kudi Naira N100,000 domin ci gaba da ayyukan jin kai da taimakon al’umma.

Da yake jawabi bayan ganawar, ya jaddada kudirin shugabancinsu na inganta hadin kai, tallafa wa kungiyoyin al’umma da kuma yin aiki tare da duk wata kungiya mai sahihanci da ke fafutukar kawo ci gaba da kyakkyawan shugabanci a Karamar Hukumar Zaria.

Ya kuma sake tabbatar da shirinsa na ci gaba da ba da goyon baya ga dukkan kungiyoyin da ke aiki domin cigaban Zaria da nasarar Jam’iyyar APC a kowane mataki a Zaria.

𝐒𝐀𝐊𝐀𝐓𝐀𝐑𝐄𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐀𝐌𝐀𝐑 𝐇𝐔𝐊𝐔𝐌𝐀𝐑 𝐙𝐀𝐑𝐈𝐀 𝐓𝐀 𝐁𝐔𝐊𝐀𝐂𝐈 𝐀𝐋’𝐔𝐌𝐌𝐀 𝐒𝐔 𝐌𝐀𝐘𝐀𝐑 𝐃𝐀 𝐇𝐀𝐍𝐊𝐀𝐋𝐈 𝐊𝐀𝐍 𝐌𝐔𝐇𝐈𝐌𝐌𝐀𝐍 𝐀𝐘𝐘𝐔𝐊𝐀𝐍 𝐆𝐔𝐃𝐀𝐍𝐀𝐑𝐖𝐀 𝐌𝐀𝐈𝐌𝐀𝐊𝐎𝐍 𝐒𝐇𝐈𝐑𝐘𝐄-𝐒𝐇𝐈...
10/06/2026

𝐒𝐀𝐊𝐀𝐓𝐀𝐑𝐄𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐀𝐌𝐀𝐑 𝐇𝐔𝐊𝐔𝐌𝐀𝐑 𝐙𝐀𝐑𝐈𝐀 𝐓𝐀 𝐁𝐔𝐊𝐀𝐂𝐈 𝐀𝐋’𝐔𝐌𝐌𝐀 𝐒𝐔 𝐌𝐀𝐘𝐀𝐑 𝐃𝐀 𝐇𝐀𝐍𝐊𝐀𝐋𝐈 𝐊𝐀𝐍 𝐌𝐔𝐇𝐈𝐌𝐌𝐀𝐍 𝐀𝐘𝐘𝐔𝐊𝐀𝐍 𝐆𝐔𝐃𝐀𝐍𝐀𝐑𝐖𝐀 𝐌𝐀𝐈𝐌𝐀𝐊𝐎𝐍 𝐒𝐇𝐈𝐑𝐘𝐄-𝐒𝐇𝐈𝐑𝐘𝐄𝐍 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀𝐅𝐈 𝐆𝐀 𝐌𝐔𝐓𝐀𝐍𝐄 𝐊𝐀𝐃𝐀𝐍

A yau, Sakataren Karamar Hukumar Zaria, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga) ya karbi tawaga da mambobin Kungiyar Bachirawa Support Group daga Bayan Cinema a ofishinsa.

Kungiyar ta ziyarci Sakataren ne domin gabatar da koke-kokensu dangane da rabon tallafi da Kakakin Majalisar Wakilai, Governor Senator Uba SaniRt. Hon. Dr. Abbas Tajudeen, ya gudanar a Zaria.

Yayin da yake jawabi ga tawagar, Sakataren ya yaba da wannan kokari na Kakakin Majalisar, amma ya yi kira ga mambobin kungiyar da daukacin al’ummar Zaria da kada su dauki wadananan tallafin a matsayin ma’aunin ci gaba.

Ya jaddada cewa babban nauyin gwamnati shi ne samar da ci gaba mai daurewa da tsare-tsare masu anfani ga kowa da kowa, ba wai raba tallafi kadai ba wanda kan iya haifar da rarrabuwar kai da rashin gamsuwa a tsakanin jama’a.

Sakataren ya ce, “Wadannan tallafe-tallafe ba za su taba gamsar da dukkan al’ummar Zaria ba. Maimakon haka, za su iya haifar da rudani da kiyayya ga gwamnati domin wadanda ba su ci gajiyar shirin ba za su dinga zargin gwamnati. Hakikanin ci gaba shi ne lokacin da hanyoyi, asibitoci, makarantu, ruwa da wutar lantarki suke anfani ga kowa da kowa, ba ga wasu tsirarun mutane ba.”

Daga nan sai ya bayyana manyan ayyukan ci gaba da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Dr. Abbas Tajudeen, da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, s**a samar a Zaria karkashin gwamnatin APC.

Fannin Ilimi

• Aikin Zaria Education City mai darajar Naira biliyan 80, wanda zai kunshi jami’a, School of Health, cibiyoyin koyar da ilimi da nazarin shari’a, kwalejin noma da kiwon dabbobi, makarantar wasanni, kwalejin koyon sana’o’i da fasaha, cibiyar horas da shugabanci da cibiyar bunƙasa mata.
• Kaddamar da sabbin cibiyoyi a Nuhu Bamalli Polytechnic, haɓaka Federal College of Education, kafa College of Health Sciences, National Open University Campus da College of Legal Studies.
• Shirin tallafin karatu ga dalibai 30,000 wanda ya kai darajar Naira biliyan 5.
• Tallafin karatu cikakke ga ɗalibai 250 na NILEST.
• Gyaran makarantu firamare da sakandare guda 116.
• Gina sabbin dakunan kwanan ɗalibai maza da mata a NILEST.

Fannin Lafiya

• Gina da kaddamar da Asibitin Kwararru mai gadaje 100 a Zaria tare da goyon bayan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
• Kammala cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko masu gadaje 20 da cibiyoyin koyon sana’o’i a Kakiyeyi, Gwargwaje Kufena, Jushi, Rubuchi, Yeskwake, Anguwan Kaya, Gabari da sauran al’ummomi.

Ababen More Rayuwa da empowerment:

• Gina da gyaran gadojin Agoro, Kofar Doka, Abba da Nagoyi.
• Gina kasuwar Zaria City Market mataki na daya da na biyu a Amaru.
• Gyaran Nasara Stadium da Malam Musa Hall.
• Raba taraktoci, takin zamani, motoci 117, adaidaita sahu 200 da babura 1,000 ga manoma, matasa da masu sana’ar sufuri.
• Tallafin kudi kai tsaye ga mutane 2,400.
• Bai wa matasa 800 da aka horar tallafin Naira 250,000 kowannensu.
• Bai wa kananan da matsakaitan ’yan kasuwa 1,600 tallafin Naira 100,000 kowannensu.
• Alkawarin samar da asusun Naira miliyan 100 ga wadanda s**a kammala koyon sana’o’i.

NASARORIN GWAMNA UBA SANI A ZARIA DA JIHAR KADUNA

Hanyoyi da Ababen More Rayuwa

• Kammala t**in Dogon Bauchi zuwa Kakiyeyi zuwa River Galma mai tsawon kilomita 35 a Karamar Hukumar Zaria.
• Kammala t**in karkara na Hanwa zuwa Agoro zuwa Hanga Ruga wanda ya kawo ƙarshen matsalar sufuri da aka dade ana fama da ita.
• Kammala ayyukan inganta titunan Magajiya zuwa Kasuwan Amaru da Audi zuwa Kano Road a Zaria.
• Kaddamar da aikin sake gina hanyoyin cikin Ahmadu Bello University masu tsawon kilomita 60 tare da magudanan ruwa, fitilun t**i da hanyoyin masu tafiya a kasa.
• Gudanar da ayyukan hanyoyi 78 masu tsawon kilomita 775 a kananan hukumomi 23 na jihar.

LAFIYA:

• Habaka cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 255 zuwa mataki na biyu a fadin jihar Kaduna.
• Sake gina manyan asibitoci guda 12 da kafa cibiyoyin ƙwarewa guda 23.
• Kaddamar da Asibitin Renewed Hope mai gadaje 100 a Zaria tare da ci gaba da ayyukan cibiyoyin kwarewa a Babban Dodo da Chikaji.

Wutar Lantarki da Ruwa

• Samar da transformers 600 da solar streetlights 10,000 a fadin jihar.
• Zaria, Sabon Gari da Kudan sun amfana da rabon transfoma da dama.
• Samar da megawatt 8 na wutar lantarki ga Ahmadu Bello University ta hanyar yarjejeniya da Hukumar Rural Electrification Agency a watan October 2025.
• Farfado da fannin ruwa ta hanyar shirin Naira biliyan 100 wanda ya hada da biyan bashin Naira biliyan 1.3 da dawo da wutar lantarki ga matatun ruwa.

Ilimi da Noma

• Gina sabbin makarantun sakandare guda 62.
• Samar da dakunan karatu 2,326 da kujeru 30,742.
• Ƙara kasafin kuɗin noma daga Naira biliyan 1.48 a shekarar 2023 zuwa sama da Naira biliyan 74 a shekarar 2025.

A karshe, Sakataren ya sake jaddada aniyar Karamar Hukumar Zaria karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar na ci gaba da goyon bayan manufofi da shirye-shiryen da ke kawo ci gaba mai ɗorewa ga al’umma maimakon waɗanda za su haifar da rarrabuwar kai. Ya kuma yi kira ga Bachirawa Support Group da sauran masu ruwa da tsaki da su rungumi manufar APC ta gina Zaria ta hanyar samar da hanyoyi, inganta lafiya, ilimi da wutar lantarki, wadanda su ne ginshika ci gaba na gaskiya.

𝐙𝐀𝐑𝐈𝐀 𝐂𝐎𝐔𝐍𝐂𝐈𝐋 𝐒𝐄𝐂𝐑𝐄𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐑𝐄𝐂𝐄𝐈𝐕𝐄𝐒 𝐕𝐀𝐑𝐈𝐎𝐔𝐒 𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏𝐒, 𝐇𝐎𝐍𝐎𝐑𝐄𝐃 𝐙𝐀𝐌𝐑𝐔 𝐈𝐍𝐕𝐈𝐓𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍, 𝐒𝐔𝐏𝐏𝐎𝐑𝐓𝐒 𝐑𝐈𝐒𝐈𝐍𝐆 𝐒𝐓𝐀𝐑 𝐅𝐎𝐔𝐍𝐃𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍 𝐖𝐈𝐓𝐇 𝐍𝟓𝟎,𝟎𝟎𝟎T...
10/06/2026

𝐙𝐀𝐑𝐈𝐀 𝐂𝐎𝐔𝐍𝐂𝐈𝐋 𝐒𝐄𝐂𝐑𝐄𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐑𝐄𝐂𝐄𝐈𝐕𝐄𝐒 𝐕𝐀𝐑𝐈𝐎𝐔𝐒 𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏𝐒, 𝐇𝐎𝐍𝐎𝐑𝐄𝐃 𝐙𝐀𝐌𝐑𝐔 𝐈𝐍𝐕𝐈𝐓𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍, 𝐒𝐔𝐏𝐏𝐎𝐑𝐓𝐒 𝐑𝐈𝐒𝐈𝐍𝐆 𝐒𝐓𝐀𝐑 𝐅𝐎𝐔𝐍𝐃𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍 𝐖𝐈𝐓𝐇 𝐍𝟓𝟎,𝟎𝟎𝟎

This evening, the Secretary of Zaria Local Government, Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), continued his engagement with various groups and individuals as part of his commitment to an open-door policy and grassroots development.

Among those received was the Aminiyya Mobilization Network, founded by Aminu Zaria, Executive Director/Chief Executive of the Nigerian Integrated Water Resources Management Commission (NWRMC). The Zaria Chapter delegation, led by its Coordinator, Hon Shehu Tsatsoriba, visited to formally introduce the local chapter to the Council Secretary.

The Secretary also honored an invitation from the Zazzau Motorcycle Riders Union (ZAMRU), where members appreciated his continued support for their activities and reaffirmed their support for Governor Senator Uba Sani, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, and all APC candidates in Zaria.

As part of his community engagements, The Secretary visited Baba, popularly known as Baka Roshin, who sustained injuries in an accident some months ago, and prayed for his speedy recovery.

Later in the evening, members of the Rising Star Foundation paid him a visit and honored him with the position of Patron after he advised them on self-reliance and youth development. To support the foundation’s activities, he donated N50,000.

Signed:
Hassan Zakariyya
Personal Assistant, Media and Communication to the Council Secretary, Zaria Local Government

Address

Zaria Local Government Sectariat
Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when The Secretary Zaria LG posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share