07/07/2023
Abubuwa 5 da Suke janyo Bala'i Acikin Al'umma
Hadisi Ya Tabbata daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya ƙara masa yarda)
Yace Watarana muna zaune sai ga Manzon Allah (S.A.W) yazo wucewa, Yace " ya ku taron muhajirai! Akwai wasu abubuwa guda 5 idan al'umma s**a Jarabtu dasu!
Ina Roƙon Allah kada ku riske wannan Lokaci.
1⃣ Duk Al'ummar da s**a bayyana Alfasha! Tabbas zasu samu kansu cikin Annoba da yaduwar sabbin cututtukan da ba'a taɓa ganin su ba!
2⃣ Duk Al'ummar da suke tauye modu da sikeli! Tabbas zasu samu kansu cikin yanayi na fari (rashin ruwan sama), Tsadar Rayuwa da cutarwa daga azzaluman Shuwagabanni.
3⃣ Duk Al'ummar da s**a hana zakkar dukiyoyinsu! Tabbas Allah zai hanasu ruwan sama! Idan kaga Ruwa, an yine kawai saboda yara da dabbobi da suke rayuwa a cikinsu.
4⃣ Duk Al'ummar da s**a saɓa alkawarin Allah da Manzon sa! Tabbas Allah zai ƙasƙantar dasu a gaban abokan gabansu.
5⃣ Duk Al'ummar da Shuwagabaninsu basu hukunci da Littafin Allah, kuma suke chanza Abinda Allah ya sauƙar! Tabbas Allah zai sanya gaba, yaƙi da ganin Aibin Junansu a tsakaninsu.
Ibn Majah ne ya Rawaito Wannan Hadisin.
Dan Girman Allah acikin Waɗannan Abubuwa 5 wanne ne ba'a aikatawa a Nigeria? A hakan kuma muke jiran ganin dai dai
Telegram
👇👇
https://t.me/karatun_malaman_sunnah