23/07/2022
Wai Laifin Me Al'ummar Gundumar Gwangwan S**a Yi Wa Gwamnatin Kano Ne?
..ba hanyoyi, ba makarantu, ba da ba din ma ba su misaltuwa
Al'ummar gundunar Gwangwan dake Karamar Hukumar Rogo a jihar Kano, hakika wannan al'umma dake cikin garin Gwangwan da kewaye suna cikin mawuyacin hali duba da yadda matsaloli rashin ababen more rayuwa s**a yi wa yankin katutu.
Duk wanda ya san garin Gwangwan ya san gari ne mai tarin al'umma da garuruwa kewaye da shi masu tarin yawa. Amma ku dubi zahirin yadda hanyar yankin garuruwan suke ciki, inda a haka ake jigila da mata masu ciki da marasa lafiya a wannan hanyar.
Haka kuma hanyar suke bi domin neman abincinsu wato Kasuwancinsu. Kuma Gwamanti tare da wakilanta sun san halin da wannan yanki yake ciki amma ta yi shiru ba ta waiwaye su ba.
Akalla wannan lalacewar hanyar tun shekarar 2015 take amma abin sai cigaba yake.
Yana da kyau a tausayawa mutanen wannan yanki domin ganin su ma sun sami jin dadi da walwala. Domin lalacewar hanyar nan ba karamar barazana ba ce ga al'ummar wannan yanki musamman idan aka ce damuna ta yi jama'a har tsoran bin hanyar suke yi.
FANNININ KIWON LAFIYA
Gaba daya wurin da ake kula da lafiyar al'ummar yankin Gwangwan da sauran kauyuka dake kewaye gaba daya shi ma ya sami matsala, iska ta yaye kwanon, ruwa yana shiga ciki.
Sannan ba kayan aikin da za a kula da marasa lafiyar, haka kuma babu ingattattun ma'aikatan da za su kula da marasa lafiyar yadda ake bukata.
FANNIN ILMI
Makarantar firamare ta Gwangwan
ita ma ruwa da iska ya yaye kwanon, ginin ma ya rushe.
Kai matsalolin ba za su misaltu ba, domin idan muka ce za mu jero su sai dauki tsawon lokaci.
Muna rokon Gwamnatin jihar Kano da dan majalisar tarayya mai wakiltar Rogo da Karaye da dan majalisar jiha mai wakiltar Rogo da shugaban karamar hukumar Rogo da sauran magabatan Gwamnatin da su duba wannan koken Bayin Allah na yankin Gwangwan.
Daga Bashir Mainaseebii GwanGwan Rogo , Kano