31/05/2022
Yadda tafiyar farko na jirgin Titanic dauke da fasinjoji ya kasance. Amsar Tambayar Nafisa Auwal Auwal
RMS Titanic jirgin fasinja ne na Burtaniya, wanda ke karkashin layin White Star Line, wanda ya nutse a Arewacin Tekun Atlantika a ranar 15 ga Afrilun 1912 bayan ta bugi wani dutsen kankara a lokacin balaguron farko da ta yi daga Southampton, UK, zuwa birnin New York.
RMS Titanic shi ne jirgin ruwa mafi girma da ke shawagi a lokacin da ta shiga sabis kuma na biyu na manyan jiragen ruwa uku na Olympics da ke karkashin Kamfanin White Star Line. Kamfanin jirgin ruwa na Harland da Wolff ne s**a gina ta a Belfast . Thomas Andrews, wanda shi ne babban hafsan sojan ruwa na tashar jirgin ruwa a wancan lokacin, ya mutu a cikin bala'in.
Jirgin ruwan Titanic ya samu albarkar manya da kuma shahararrun injiniyoyin fasaha da kere-kere na wancan zamani. Akwai mutum uku da s**a dauki nauyin zana tsari da kira da kuma yanayin rayuwar wannan jirgi. Na farko shi ne Lord Pirrie, wanda darakta ne a kamfanin Harland Wolff da White Star Line. Sai wani kwararren mai zanen jiragen ruwa mai suna Architect Thomas Andrews, wanda shi ne manajan kere-kere na kamfanin, wato Construction Manager kenan. Sai na ukun su mai suna Alexander Carlisle, wanda ya kasance babban manajan ma’aikatan kera jirgin ne baki daya (Shipyard General Manager).
A Ranar 10 ga watan Afrailu ne dai jirgin RMS ( Royal Ship Mail ) RMS ya tashi daga babbar tashar jirgin ruwan birnin Southampton na kasar Ingila don zuwa birnin New York da ke kasar Amurka. Da ya dauko hanya sai yayi zango a tashar jirgin ruwa na Cherbourg da ke kasar Faransa, inda ya kara daukan wasu fasinjoji. Bayan wannan tasha, ya sake dakatawa a tashar Queens Town ta kasar Ailand, nan ma ya kara wasu fasinjojin. Duk da cewa ba kai tsaye ya dauki mutane a wannan tasha ba, saboda nauyin jirgin da girmansa sun sha karfin gabar tekun. Don haka da yazo daidai tashar, sai aka saukar da kananan kwale-kwale, aka kwaso fasinjojin da suke son tafiya. Dubi yadda aka kera jirgin ruwan Titanic..
Daga wannan tasha ta Queens Town, jirgin bai kara dakatawa a kowace tasha ba, sai tafiya babu k**a hannun yaro. A wannan lokaci jirgin ya dauki mutane 2,227 ne; tsakanin matuka jirgin, da ma’aikata, da injiniyoyi da kuma fasinjoji. Shugaban matuka jirgin gaba daya shi ne Captain Edward J. Smith. Bayan haka, akwai babban daraktan kamfanin White Star Line a cikin tafiyar, wato J. Bruce Ismay, sai kuma wanda ya shugabanci kera jirgin baki daya, wato Thomas Andrews. Daga cikin fasinjojin da ke cikin wannan jirgi, akwai ‘yan kasuwa, da shahararrun ma’aikatan banki, da kuma kasaitattun masu kudin kasar Ingila da Amurka da kasar Ailand.
Kudin fasinjan da ke matakin farko, wato First Class, shi ne dala 4,350 ($4,350), wanda aka kiyasta kimarsa da kimar dala a shekarar 2008 ya kai dala 95,860 ($95,860).
Bayan ya kwashe kwanaki hudu yana tafiya dare da rana safe da yamma, a daren kwana na biyar ne Captain Edwards ya fara samun sakonni daga hanyar sadarwa ta rediyo dake jirgin, cewa akwai curin tsaunin kankara a gabansu, wato Iceberg. Amma sai bai damu ba. Ana cikin tafiya, sai ma’aikatan da aka wakilta su rika lura da tafarkin da jirgin ke bi, wato Lookouts, s**a hango wannan tarin kankara a gabansu. Nan take s**a sanar da masu lura da cibiyar sadarwa, inda su kuma s**a fara watsa sakonni kan wannan lamari. Captain Edwards na jin haka, sai ya bayar da umarnin cewa a rage Gudu, sannan a juya akala zuwa bangaren hagu.
To amma wannan bayani bai zo da wuri ba. Kafin su gama juya akala, nan take wannan tsaunin kankara ya gurji mazaunin jirgin daga kasa, wato Hull kenan. Hakan ya sabular da karafan da ke rike da mazunin jikin jirgin, inda ruwa ya fara shiga nan take babu kakkautawa. Lokacin da Captain Edwards ya ga haka, sai ya sa aka fara rufe farfajiyar kasan jirgin, wato wurin da aka tanada don zuba kayayyaki kenan. Amma saboda tasiri da karfin wannan ruwa da ya fara shigowa, kafin a rufe sauran, guda hudu daga cikinsu sun fara cikewa da ruwa. Wadancan bututu guda takwas da aka tanada don amayar da ruwa sai s**a fara aikinsu, inda s**a ta amayar da ruwan zuwa waje, ta baya. Sai dai kuma kash, saboda girman jirgin, da kuma yawan ruwan da ke tudadowa daga gaba inda aka samu huji, wadannan bututun amayar da ruwa sun kasa amayar da ruwan cikin lokaci guda.
Nan take kasan jirgi ya fara cikewa, sai cikin dakunan mutane, sai hawa na sama. Ana cikin haka sai jirgi ya fara nutsewa ta baya, saboda tasirin ruwan da ke makare a kasansa. Wannan tasa sai kan jirgin ya daga sama, inda a karshe ya tsage ko ya karye a tsakiya; bangaren bayan ya yi kasa cikin teku, kan kuma ya zauna a sama. Kafin lamarin ya kazance haka, nan take sun fara aikawa da sakonnin neman agaji. Ana cikin haka sai ga wasu jirage s**a kawo dauki. To amma saboda kananan kwale-kwalen ceto, wato Lifeboats, da jirgin ya ke dauke dasu basu kai yawan mutanen da ke cikin jirgin ba, haka wasu s**a nutse cikin ruwa, s**a mace. Wasu kuma aka ceto su da kyar.
Bayan an gama tsamo wadanda s**a mutu da masu rai, a karshe dai mutun 1,517 ne s**a mutu. Hakan ya faru ne a daren 15 ga watan Afrailu, 1912. Wannan shi ne mafi munin hadarin jirgin ruwa da aka yi a shekarar, kuma yana cikin hadarurrukan da aka yi da s**a haddasa sauye-sauye a dokokin tafiyar da jiragen ruwa na duniya, wato International Maritime Laws.
Daga cikin dalilan da aka ta cewa sun haddasa wannan hadari dai akwai yawan gudu. Wannan shi ne sak**akon da gungun masu bincike da kasar Ingila ta kafa ya tabbatar. Cewa jirgin na gudu ne fiye da kima, don haka ya samu matsala wajen juyawa a lokacin da aka hango wancan tsauni na kankara. Wasu masu binciken kuma s**a ce ruhin jirgin ne ke da matsala, wato Rudder kenan a turance. Shi wannan ruhi dai shi ne mai nuna wa jirgin ruwa inda zai dosa; k**ar dai kwakwalwarsa kenan.
Copy