24/07/2022
ILIYA DAN MAI KARFI(1)
ABIN AL AJABI
A wani gari can cikin kasashen Gabas, an yi wani ana kiransa Sahabi, da matarsa wai ita Murjanatu. Suna zaune cikin gidan gona. Ba wadansu wadatattu ba ne sosai, amma kuma ba matalauta ba ne. Suna da yan dabbobi da gonaki. Abin da dai ya rage musu jin dadin zaman duniya shi ne rashin magaji kawai. Allah bai nufe su da samun da ba.
Shekara da shekaru suna ta neman haihuwa, amma ba su samu ba. Ran nan kwanci tashi, sai Murjanatu ta sami ciki. Wai kada ka so ka ga irin murnar da Murjanatu da Sahabi s**a yi. Tun cikin yana da wata hudu, Sahabi ya soma tanadin iccen biki.
Ran nan da rana tsaka, Sahabi yana aiki a bayan gida, cikin gona, sai ya ji an rafsa guda, Ayyururui! Ayyururui! , har sau uku. Sahabi ya jefad da fartanya, ya sheko da gudu cikin gida. Da zuwansa kuwa ya tarar da abin da ya ke fata ya gani. Murjanatu ta sauka, ta sami da, namiji, santilo. Da ranar ta kewayo, jama a s**a taru, aka rada wa jaririn suna Iliya.
Ana nan har yaro ya kusa isa yaye, sai rashin lafiya ya same shi, kafafuwansa duka biyu, da hannu guda, s**a shanye. Shi ke nan ya zauna a haka, har ya girma. Daga kan dan gadonsa ba ya iya fita ko ina, sai dai am fita da shi. Iyayensa s**a yi bakin ciki kwarai, s**a hakura.
Wata rana iyayen Iliya sun tafi gona, ba kowa gidan sai shi kadai, kan gadonsa, yana ta tunanin yadda duniya ta ke, yan kulle-kullen abubuwan da zai yi, da yana da kafafu. Kwanfa, sai ya ji an yi sallama, Salamu alaikum, salamu alaikum! Sai Iliya ya amsa, Alaikas salamu. Kowane ne ya shigo! Sai ga wadansu mutane su uku, suna sanye da tufafi irin na aLarabawa, sun yi shigar alhazai. Ko wannensu yana rike da doguwar tasbaha, yana ja. S**a zauna. Iliya ya yi musu maraba, s**a amsa masa da murna.
Iliya ya dubi mutanen nan da kyau, ya ga ba irin mutanen da ya saba gani ba ne. Sai ya zaci ko irin mutanen nan ne da ya kan ji ana cewa suna bi gari gari sun