18/08/2026
Haihuwar Manzon Allah SAW
An haifi Manzon Allah SAW ranar litinin 12 ga watan Rabi'ul Awwal a shekarar giwaye.
A daren da aka haifi Manzon Allah SAW, abubuwan mamaki sun bayyana. Daga cikin su akwai:
Kakkaryewar gumaka duk s**a faɗi akan fusakun su. Haske ya bayyana a tare dashi kuma wannan hasken seda ya haska benayen sham, kuma katangun Kisra ta tsatstsage kuma wutar da suke bauta ta mutu alhali bata taba mutuwa ba kafin lokacin, hakanan ƙoramar sawata itama ta qafe.
Ibn Abbas yace: An haifi Manzon Allah SAW ranar litinin, an aiko shi da Manzonci ranar litinin kuma yabar Makkah zuwa Madinah ranar litinin kuma yayi wafati ranar Litinin kuma ya ɗaga dutsen Aswad ranar litinin kuma an haifeShi da shayi kuma cibin sa a yanke SAW babu ƙazantar haihuwa a tare dashi se haske da ya haskaka ko ina.