19/11/2024
ALLURAR FENTA WATO (PENTAZOCINE)
Allurar Tana Cikin Rukunin Magungunar Da Ake Kira (Narcotic Analgesic ) Wanda Aka Kirkireta Domin Matsanancin Zafin Ciwo kamarsu:- Radadi,Zugi Adalilin,
1.Murdewar Hanji
2.Ciwon Baya
3.Karaya Dss
Akanyi Allurar A Sassan Jiki Kamar Su ,
1.Im, ---A Tsoka Ta karshe
2.Sub, ----A Tsoka Na 2
3.Iv,--A jijiya ,
Ya Dan Ganta Da Yanayin Ciwon Da Likita Yake Bukatar Yinta ,
Tanada Wasu Illar Da Ake Fuskanta Bayan Yinta wanda baya Cutarwa Ga Dan'adam Kamar:-
1.Amai
2.Ganin Jiri
3.Mutwar Jiki , Barci Dss.
Idan Akayiwa Mutum Allurar kwalba Daya Yana Iya kwashe Awa 6 yana Barci batare Da Yafarkaba ko kasa da hakan,
ILLOLINTA GA RAYUWAR DAN ADAM KAI TSAYE.
1.Wanda Yafara Yinta Yana Wuya Yadaina.
2. Tana Haifar Da Cancer A Cikin Jini, Duk Wanda yadade yana Yinta jininsa Zai Lalace Wanda ko wane lokaci yana iya rasa Rayuwarsa.
3.Tana Haifar Da Zautuwa,Dimuwa,Makuwa,Mantuwa Hauka Kaga Babu Maganar Ibada Kenan kwata-kwata.
4. Tana Lalata Sinadarin Haihuwa Anan kuma Anbar Sunnar Ma'aiki,
5.Tana Dauke Al'ada Ga Ya Mace,
6.Matsanancin Rashin Bahaya.
7. Lalacewar Hanji.
8.Tana Haifar Da Matsala A Kunhu Wanda ke Zarcewa Ga Sarkewar Numfashi ,
9. Bugawar Zuciya
10. Kara Radadin Ciwo Ga Wanda Yasaba Anfani Da ita etc...
Dukkan Wannan Illoli Suna faruwane Ga wanda Ya Dauketa Kamar Abinci. Zaka Samu Matashi Yana Iyayin kwalba 5,6,10 Arana Guda Da Sunan Yana Chaji , Inada Tabbacin Da Matashi yasan Wannan Illolin Da Ya kiyayeta Tunda Sauran Kuruciyarsa ,
Muna Kira Ga Masu Ta'amali Da Iren-Iren wannan Miyagun Kwayoyi Da Suyi Gaggawar Dainawa Ko Zasu Tsira Da Lfyarsu Da Mutuncinsu Acikin Al'unma,
Sannan Gobnati Yakamata Shiga Cikin Lamarin Musanman Mutanen Dake Saidata Ba Bisa Ka'idaba
Wanda Mukayi Wannan Kira Dominsu Allah Ya Basu Ikon Gyarawa.