05/08/2026
Ur welcome
QUNGIYAR GOMBE TA MALAM CE
Ƙarƙashin Jagorancin Ubangidan Fita Kunya, Ayatullahi Tage
Muhammad Yusuf ✍️
MUNA YIWA BABANGIDA VENTURES GOMBE BARKA DA DAWOWA TAFIYAR PROFESSOR ISA ALI PANTAMI A JAM'IYYAR PDP.
Muna mika saƙon taya murna da maraba ga Babangida Ventures Gombe bisa matakin da ya ɗauka na komawa tafiyar Professor Isa Ali Pantami a jam'iyyar PDP. A siyasa, mutane na da 'yancin yin zaɓin da s**a ga ya dace da ra'ayinsu da abin da suke ganin zai amfani al'umma.
Abin da ya fi muhimmanci a wannan tafiya shi ne hangen nesa na samar da ci gaba, haɗin kai da bunƙasa rayuwar matasa. A shekaru da s**a gabata, Professor Isa Ali Pantami ya kasance ɗaya daga cikin fitattun shugabannin da s**a yi kira ga matasa su rungumi ilimi, fasaha da kirkire-kirkire domin su dogara da kansu.
Daya daga cikin abubuwan da s**a fi daukar hankali a tafiyarsa shi ne ƙarfafa matasa su shiga duniyar Digital Skills. Wannan ya haɗa da koyon fasahohin kwamfuta, shirye-shiryen kwamfuta (programming), tsaron bayanai (cybersecurity), kirkirar abun ciki (content creation), amfani da fasahar zamani wajen kasuwanci, da sauran dabarun da ke ba matasa damar samun aikin yi ko ƙirƙirar nasu sana'o'i.
A yau duniya ta koma ta fasaha, kuma duk al'ummar da ta ba matasanta ilimin zamani za ta fi samun ci gaba. Saboda haka, zuba jari a ilimi da fasahar zamani ba kawai anfani ne ga mutum ɗaya ba, har ma ginshiƙi ne na ci gaban jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.
Muna kira ga duk masu kishin ci gaban Gombe da su ci gaba da tallafa wa manufofin da ke ƙarfafa ilimi, zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasa tattalin arziki. Mu guji kalaman da za su raba kan al'umma, mu fifita tattaunawa mai amfani da haɗin gwiwa.
Allah Ya ba mu shugabanci nagari, Ya haɗa zukatan al'umma, Ya kuma ba matasanmu damar cin gajiyar ilimi da fasahar zamani domin gina makoma mai kyau.
QUNGIYAR GOMBE TA MALAM CE
Ƙarƙashin Jagorancin Ayatullahi Tage