13/03/2023
WACECE MACE MAI KYAU ¿.
A al’ada ta dan Adam yana son tufafi mai kyau domin ya sani tufafi mai kyau yana kara wa mutum kima da martaba hakan ne ya sa shi sanya tufafi mai kyau da zai kayatar tabbas akwai damar zaben tufafi mai kyau kuma hakan ba laifi ba ne shi ya sa ake cewa idan kana da kyawu to ka kara da wanka to haka ita ma mace take ana so ta zama mai kyau domin ba lallai ba ne sai an auri mummuna ko wata burtuntuna don haka lura da kyawu din ba laifi ba ne amma kyawu iri biyu ne:
Akwai kyawu na zahiri.
Akwai kuma na badini.
Abin da aka fi so shi ne ya zamana an hada duka biyun saboda shi kyawu na zahiri yana dusashewa matukar babu kyau na badini sai ya zama tamkar na wucin gadi ne domin cikin kankanen lokaci zai koma tamkar na dan maciji ka ga dan maciji ai yana da kyau zai rika sheki gwanin ban sha’awa don haka idan ba kida kyawu to ki tabbata kin mallaki kyawun badini hakan zai taka rawa wurin dauwamar da kimarki a zuciyar abokin zamanki Kada ki kasance don kina da kyawu amma kuma ki rika sarin mijinki wadansu mazan sun fi son fara kyakkyawa wadansu kuma sun fi son baka kyakkyawa hausawa suna cewa Ido wa ka raina ¿ Sai yaka ce wanda nake gani kullum domin duk kyawun ki daga kin yi aure yau da gobe mijinki zai daina ganin kyawunki abin da zai rage har kuma ya rika ba ki daraja a wurin mijinki shi ne Kyawun hali domin idan kyawu na zahiri ya hadu da kyawun hali da kuma kyautatawa to wannan ne zai ba mutum kariya wajen ganin wancan kyawu kullum yana nan a lokacin da kika
rika kyautata wa mijinki kyawunki ba zai gushe ba amma a lokacin da kika munana wa mijinki to komai kyawunki na zahiri sai ya gushe a idanu da kuma zuciyar mijinki saboda duk lokacin da mace ta munana wa mijinta to bakikkirin zai rika ganin ta zai ga babu wani annuri a tare da ita mace kamila ita ce wacce idan mutum ya kalle ta zai samu natsuwa kamar yadda Amirul Mumina Ali yake cewa: “Na kasance da na kalli Fatima Azzahra sai inji damuwa da bakin ciki sun tafi.” Saboda ita Fatima ta hada duka