18/08/2024
Tattaki gaba da lokaci: Labarin Paul Dienach, wanda ruhinsa ya rayu a shekara ta 3906 AD.
SADIQ TUKUR GWARZO
Paul Amadeus Dienach wanda aka haifa a shekarar 1884 AD kusa da birnin Zurich, farfesa ne a harshen Faransanci da Jamusanci, wani muhimmin abu ya taɓa aukuwa dashi mai ban mamaki.
An soma wallafa Labarinsa ne a harshen Girkanci a shekarar 1972 AD, da hannunsa ya rubuta abubuwan da ya iya kiyayewa bayan farfaɗowarsa daga dogon suma na tsawon shekara ɗaya, a inda ruhinsa yayi nasarar tafiya gaba da lokaci, har ya rayu a shekara ta 3906 AD.
Ɗalibin Paul Dienach, mai suna Papahatzis, wanda ya zama Farfesa a fannin sharia, shine wanda ya fassara labarin da Paul ya aike masa daga Jamusanci zuwa harshen Girkanci, ya bayyana Dienach ɗin a matsayin mutum mai tsantseni da kamewa. An k**anta cewa Paul Dienach ya rasu bayan doguwar jinya daga cutar Tarin Fuka a birnin Athens na ƙasar Girka ko kuma akan hanyarsa ta dawowa gida daga ƙasar Italy, a farko-farkon shekarar 1924 AD.
An ƙiyasta cewa Paul Dienach ya jamu da wata lalurar ƙwaƙwalwa mai suna 'encephalitis lethargica'. A lokaci na farko daya fara bacci bayan kamuwa da cutar, ya samu farkawa bayan tsawon mintuna 15, amma a zagaye na biyu, bai farka ba sai da ya shafe tsawon shekara ɗaya a wani yanayi da za a iya kira da suna 'dogon suma'. Bayan farkawar sa ne, Dienach yayi iƙirarin cewa ruhinsa ya samu yin tattaki gaba da lokaci, har ma ya shiga cikin jikin wani mutum mai suna Andreas Northam, wanda ya rayu a shekara ta 3906 AD.
Da fari, Dienach ya ji tsoron sanar da mutane abinda ya hango don gudun kada ayi masa kallon mahaukaci, amma daga bisani, ya yi ritaya daga aikinsa na karantarwa a matsayinsa na Farfesa tare da rubuta cikakken labarin wannan yanayi da ya hango, a wani littafi mai shafi 800.
Dienach ya fasalta duniya da mutanen dake rayuwa a cikinta a shekarar 3906 AD gwargwadon fahimtarsa da abinda ya gani a matsayinsa na wanda yake rayuwa a ƙarni na 20. Yana da matuƙar wahala ga wanda ya rayu a shekarar 1921AD ya fahimci cigaban kimiyyar da duniya ta rabauta dashi a shekarar 2024 AD da muke ciki, b***e kuma a k**anta da wanda ya gani a shekarar 3906 AD, ana iya cewa cigaba ne marar misaltuwa.
A cikin labarin nasa, ya faɗi cewa mutanen da ya riska suna rayuwa a shekara ta 3906 AD, sun fahimci lalurar ƙwaƙwalwar da yake fama da ita, har ma suna kiranta da suna "conscious slide.".
Ya ce sun sanar dashi wasu abubuwa da s**a faru tun daga ƙarni na 21 har zuwa ƙarni na 39, amma basu sanar dashi abubuwa game da ƙarni na 20 da yake ciki ba saboda tsoron gudun sauyin rayuwarsa ko kuma rayuwar da zata gabata.
LABARIN DIENACH: TATTAKI CIKIN ZAMUNNA MASU KUSANTOWA
Dienach ya rayu a zamani mai gabatowa a matsayin Andreas Northam
A littafin da ya rubuta, ya faɗi yadda ya rayu tsawon shekara ɗaya a matsayin majinyaci a wani babban asbitin ƙasar Italiya bayan ya samu hatsari daga mota mai tashi sama a cikin shekara ta 3906.
WASU MUHIMMAN ABUBUWA DA DIENACH YA RUWAITO
Abubuwan da s**a faru tsakanin shekara ta 2000 zuwa ta 2300: Yace a waɗannan shekarun, mutanen dunigya suna ta fafutika da matsalar yawaitar mutane a duniya, da matsalar tattalin arziƙi, da gurɓacewar muhalli da rashin dai-daito wajen rabon arziƙin ƙasa da yaƙe-yaƙe tsakanin ƙasashe fami da uwa uba ƙarancin abinci.
2204: Dienach ya ruwaito cewa a shekarar 2204 AD cigaban kimiyya da fasaha a duniya ya kai yadda sama da mutane miliyan 20 ke rayuwa a duniyar Mars dake sararin samaniya. Daga nan aka samu wata gagarumar annoba wadda ta halaka ɗaukacin mazauna duniyar ta Mars. Wannan abu yayi sanadiyyar shafe tsawon shekaru ba tare da ɗan Adam ya sake muradin jarraba rayuwa a wata duniyar sararin samaniya ba.
2309: Yace a cikin wannan shekarar matsalolin muhalli dana zamantakewar ɗan Adam sun ta'azzara a duniya, hakan yayi sanadiyyar aukuwar gagarumar annoba tare da aukuwar yaƙe-yaƙen makami mai linzami a tsakanin dukkan ƙasashen duniya. Ƙasashen yammacin dunita sun mallake ƙasar China. Mutanen duniya da yawa sun rasa rayukansu a sabili da yaƙe-yaƙen mak**an ƙare dangi, sannan mutane da yawa sun yi hijira, inda s**a koma duniyar Mars da rayuwa.
2396: Wucewar waccan annobar da ta gabata ne ya yi sanadiyyar kafuwar wata gagarumar Majalisar Ɗinkin Duniya wadda ke ƙunshe da wakilan dukkan ƙasashe ba tare da tsangwama ba. A wannan majalisa, ƙarfi da fifiko ya dogara ne ga Masu ilimin kimiyya da Fasaha da Taimakon Bil'Adama. Ba a maganar kuɗi a wannan lokaci. Al'ummar duniya sun ƙaranta, don haka albarkatu sun ishi kowa da kowa. Duk da haka, za a samu ƙasashen da zasu bijerewa wannan tsarin, har kuma shekarun duhun kai su soma.
3382 A wannan shekarar, wani babban abin mamaki ya auku- watau sauyawar ƙwaƙwalwar ɗan Adam ta yadda tasrifinta ya ninku daga yadda aka sanshi zuwa wani yanayi mai suna 'hyper-vision'. Wannan ya yi silar binciko manyan ababen mamaki a wannan duniyar waɗanda ma ba a taɓa tunaninsu ba.
3400-4000: Shekaru masu daraja sun soma bayan kimanin shekaru 1000 da somawar shekarun duhun kai.
A ƙunshin Gwamnatoci da shugabancin al'umma babu maganar masana kimiyya da fasaha, sai dai wasu zaƙaƙuran fasihai da ake kira da suna 'Universal Creators'- masana ne da suke da ƙwarewa a kafanin harkokin cigaban ɗan Adam.A wannan zamani, mutum yana yin aiki ne kawai tsawon shekaru biyu a ɗaukacin rayuwarsa, watau daga sanda ɗan Adam ya riski shekara 19 da haihuwa, to zai yi wani abu kwatan-kwacin bautar ƙasa (NYSC) a masana'antun lantarki, to daga nan za a bashi laƙabin 'CIVE', watau wanda duniya ta san da zamansa. A wannan zamanin, gwamnatin duniya guda ɗaya ce, kuma ita ke kula da kimanin mutane biliyan ɗaya dake rayuwa a duniya.
Abu mafi ƙayatarwa a wannan labarin shine yadda tarihin rayuwar duniya har zuwa shekara ta 3906 AD ya tafi akan tsarin da mafi yawan masana s**a fitar na faɗi tashi da gwagwarmaya.
Rayuwar ɗan Adam a koda yaushe tana fuskantar cikas daga mabanbantan ƙalubale, wanda hakan ke silar haɗuwa da damuwa da kuma mutuwa.
Tabbas, babu wani ɗan Adam dake samun cikar burinsa ɗari bisa ɗari a wannan rayuwa, domin da zarar ɗan Adam ya cimma muradin daya sanya a gaba sai wasu muradan su sake bijirowa, sai dai kawai ga wanda ya iya gamsuwa da abubuwan daya mallaka tare da gujewa burice-buricen duniya.
Wannan labari ana iya kallonsa a matsayin hasashe kawai, abubuwan da Paul ya ruwaito na iya faruwa, suna kuma iya ƙin aukuwa. Amma idan aka kalli inda duniyar take fuskanta zuwa yanzu, muna iya cewa 'Biri yayi k**a da mutum'.