20/07/2025
Wani malamin jami'a wanda yakai matakin Dr. yana gabatar da darasi a jami'a. Da ya fara bayani, sai ɗaya daga cikin ɗaliban ya fara busa da baki (fito)!
Malamin ya yi shiru ya ce: "Wa yayi fito?"
Babu wanda ya amsa...
Ya ci gaba da bayani, sai ɗalibin ya sake yin wani fiton. Malamin ya sake tsayawa ya ce:
"Wa yayi fito?"
Amma har yanzu babu wanda ya amsa.
Ya ci gaba da karatu, amma sai ga wani fiton nan a karo na uku!
Nan fa malamin ya ajiye abin rubutu a cikin littafinsa, ya ce:
"An gama da wannan darasin! Amma zan ba ku labarin wani abu da ya faru dani a rayuwata..."
Sai ajin yayi shiru sosai, kowa ya nutsu!
"A wata rana da daddare, bacci ya ƙaurace mini, na kasa yin bacci. Sai na fita daga gida, na shiga mota ban san inda zan je ba. Ina yawo a cikin gari kawai...
Sai na ci karo da wata tsohuwa da ke ɗauke da kaya masu nauyi a kanta. Na tsaya kusa da ita, na tambaye ta ko tana buƙatar taimako. Ta yi farin ciki sosai. Na sa ta cikin mota. A hanya sai na fahimci ta sanni sosai tun da daɗewa.
Sai ta dubi idona ta ce:
"Dr., ina da ɗa wanda ba ta hanyar aure aka haife shi ba, yana karatu a jami'arku. Ina so ka zama mai karfafa masa."
Na ce mata: "Toh, amma ki faɗa min sunansa domin in san shi, kuma zan yi yadda kika roƙa."
Sai ta yi murmushi ta ce: "Za ka gane shi ko ba tare da na faɗa maka sunansa ba. Yaron ne shi mara jin magana yana da yawan fito..."
Nan take, duk ɗaliban da ke cikin aji s**a juya suna kallon wanda yake fiton!
Sai malamin ya ce masa:
"Zo nan, dan saurayi... kana tunanin na samu wannan digirin digirgir (PhD) din daga kasuwar jakuna ne?"