15/07/2026
ABIN MAMAKI A HANYAR KATSINA–ƘANKARA:
'Yan Bindiga Sun Tsayar da Motar Fasinja, Amma Abin da S**a Yi Ya Ba Kowa Mamaki
Wani bawan Allah mai suna Aliyu Ammani, U/Shanu Kaduna ya bayyana wani abin mamaki da ya faru da su yayin tafiya daga Katsina zuwa Kaduna, lamarin da ya bar fasinjojin motar cikin tsananin fargaba da rudani.
A cewarsa, direban motar ya yanke shawarar bi ta hanyar Katsina–Ƙankara, duk da cewa an san hanyar da fama da hare-haren 'yan bindiga. Wasu daga cikin fasinjojin sun nuna rashin amincewarsu, amma direban ya dage cewa babu wata matsala.
Ana cikin tafiya ne ba zato ba tsammani s**a hango wasu mutane dauke da makamai, tare da baburansu a gefen hanya, kamar yadda jami'an tsaro kan kafa shingen bincike.
Direban ya yi ƙoƙarin juyawa, amma ya makara. Sai mutanen s**a yi masa alamar ya ƙaraso inda suke.
Da motar ta tsaya, wani daga cikinsu ya tambayi direban:
"Daga ina kuke?"
Direban ya amsa: "Daga Katsina."
Sai ya sake tambaya: "Ina za ku?"
Direban ya ce: "Kaduna."
Daga nan mutumin ya ce:
"Muna neman fetur. Kuna da shi?"
Direban ya amsa da cewa babu.
Sai mutumin ya ce:
"To, ku wuce. Allah Ya kai ku lafiya."
Motar ta ci gaba da tafiya cikin shiru, kowa na mamakin abin da ya faru. Bayan sun yi nisa, wani fasinja ya yi barkwanci da direban yana cewa:
"Oga direba, idan za ka sake bi wannan hanya, ka tabbata kana ɗauke da gallon ɗaya na fetur. Zai iya zama 'rigakafin' tafiyarka!"
Mekike Tunanin ya faru a nan kuwa? Ku bayyana ra'ayinku a sashin sharhi, sannan ku bi shafinmu domin samun irin waɗannan labarai.