02/06/2023
MU DAUKI DARASIN RAYUWA
Wannan da kuke gani kwamandan yakin sojojin Nigeria ne rundina ta 130, sunansa Laftanar Kanar Umar Sani Abdulmajeed, dan jihar Katsina ne karamar hukumar Batsari
Ya taka rawa sosai wajen kwato kauyukan da Boko Haram s**a kwace a yankin Baga na jihar Borno
Idan baku manta ba, watannin baya rundinar Sojin Nigeria ta koreshi daga aiki, saboda an sameshi da laifin aikata Luwadi da kananun sojojin dake aiki karkashinsa, nima nayi rubutu a lokacin
Tsohon Soja Captain Aminu Soja idan ban manta ba kace min ka sanshi tun kana aikin soja, kuma an masa shaida da aikata Luwadi tun yana karamin Officer a gidan Soji, an sha masa nasiha amma yaki bari
Abinda zai baku mamaki jama'a shine, tun lokacin da rundinar sojin Nigeria ta kori Laftanar Kanar Umar Sani Abdulmajeed daga aiki bai komawa garinsa ba, bai sake komawa ga iyalansa da 'yan uwansa ba, kuma sai Allah Ya aiko masa da wata jinya, kusan duk abinda ya mallaka a jinya ya kare, yau juma'a Allah Ya karbi rayuwarsa ya mutu
Harsashin bindigar RPG ne ya keta masa hakarkari kamar yadda zaku gani, ance gubar harsashin ne ya saka masa cutar kansa mai kumbura jiki, bayan da aka koreshi daga aiki sai jinyar ta motsa masa sosai
Abinda zaku tambaya me ya hana wannan Kwamandan Sojoji komawa cikin 'yan uwansa bayan an koreshi daga aiki har ya mutu yau? amsar shine zai kasance kunyar duniya ne ta hanashi komawa gida? to wai dama dan Luwadi yana jin kunya ne?
Wannan babban darasin rayuwa ne 'yan uwa musamman ga 'yan Luwadi, akwai wadanda suna aikata Luwadi don neman matsayi kamar yadda bokayensu suke basu umarni, to amma ba samun duniyar ba, karshen rayuwar shine abin dubawa
Duk da ya kasance dan Luwadi, amma fa yana da kokari wajen taimakon addinin Musulunci da dukiyarsa da kuma karfin aikinsa na Soji kafin a koreshi
Addu'ah na neman gafaran Allah zamu masa ko dai mu yi shiru halinsa ya ceceshi?
Daga Datti Assalafiy