18/05/2026
Kalubalen rayuwata..
Saura kiris bom ya tashi Dani a kano.
A lokacin Da aka sanya bom Karo na biyu a kano bayan an dasa a police station sai aka sa a farm center a wannan lokaci Ina harkokina a kano ne. Kuma lokacin abokan aiki na idan zasu siya waya, memory card ko Sim suna dauka na muje.
A watarana Da bazan iya kiyaye date din ba munje farm center kuma mun kammala siyaryar da zamuyi muna fitowa katsam ji mukayi boom boom💥
Haba sai gudu kawai ake da na samu na juyo sai a raina nace Alhamdulillah da yanzu sai dai labarin mu. Tun bamu koma ba masaukin ba sai na Fara jin Kira daga mahaifana Ance bom ya tashi Amma ba inda kuke bane ko?
Ni lokacin ma kirji na buguwa yake nace kawai eh wasu friends Dina da muke 2go a wancan lokacin sai Kira kafin kace me har an datse networks din babu kira sai harbe harbe a roundabout dake kano line ohh naga takaina ranar don mun tsallake rijiya da baya
An Hana zirga-zirgi na Awa 24 Amma ni banjin dadin zama waje daya idan dare yayi na tafi zoo road kawai na fadawa wata masifar.wata masifar ce? Mu hadu a post na gaba
Gsm Village Farm Center Kano, Kano State
Zoo Road, Kano
Court Road Kano
Lawal Umar✍️