20/07/2022
Bayan Annabi Muhammadu 💞(S.A.W)💞 yayi wafati, Bilal yabar Madinah yatafi sham(Syria) sabida bazai iya rayuwa batare da Rasulullahi💞(S.A.W)💞 ba. Wani dare sai yaga Annabi Muhammadu 💞(S.A.W)💞 a cikin mafarkinsa Yana cewa "Bilal ka dauki tsawon lokaci baka kawo Mana ziyaraba". Ya farka ya hada guzirinsa yatafi Madinah inda yakira Sallah a ranan bayan tsawon kokacin da yadauka baiyi kiran Sallah ba, wohoho nan fa Madinah tarikice. Maza da mata na zubda hawaye domin tunawa da Manzon Allah 💞(S.A.W)💞 A lokacin da Bilal yakai wajan Ashahadu Anna Muhammadu Rasulullahi, sai ya Zube a Qasa cikin kuka sabida bazai juri Kiran Sallah batare da ganin Annabi 💞(S.A.W)💞 ba. Allahu Akbar!!! A lokacin da Bilal ke jinyar mutuwa yana cewa "ina cikin farin ciki matuka gobe zan ziyarci abin Qaunana Annabi Muhammadu 💞(S.A.W)💞 da Sahabban sa. Ya Allah Ka azurtamu da Soyayyan Annabi Muhammadu Rasulullahi 💞(S.A.W.)💞 da iyalansa da Sahabban sa na kwarai Ameen.
Dan Kaunar Da kakewa Annabi karaba Wannan zuwa group uku kacal💞💕💕🌹🌹